‘Yan bindiga sun yi gaba da Shugaban Ƙaramar Hukumar Takum, Boyi Manga, a Jihar Taraba.
Sun kuma harbe ɗan sandan da ke tsaron lafiyar sa, kuma su ka arce da bindigar ɗan sandan.
Wakilin mu ya samu labarin cewa an yi garkuwa da Manga wajen 12 na ranar Lahadi.
An tare shi tsakanin hanyar Chanchangi kusa da ƙauyen Agaraga, cikin Ƙaramar Hukumar Takum.
Majiyar ‘yan sanda ta ce an yi garkuwa da shi, tare da kashe ɗan sanda mai tsaron lafiyar sa, lokacin da su ke kan hanyar zuwa hedikwatar Ƙaramar Hukuma.
Har yanzu dai ba a san su wane ne su ka yi garkuwa da shi ba. Kuma zuwa lokacin rubuta labarin ba a sani ba ko masu garkuwar sun tuntuɓi iyalan sa.
Masu garkuwar sun kuma sun gudu da motar Manga, samfurin Prado SUV, da bindigar jami’in tsaron sa, ƙirar AK-47.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya ce shi ma ya ji labarin, amma har zuwa lokacin rubuta labarin nan ba a kai masa rahoton arcewa da Manga ko kisan ɗan sanda mai tsaron sa ba.