Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya karyata rade-radin da ake ta yadawa musamman a wasu kafafen yada labarai cewa wai yana maular a yi masa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a sabuwar gwamnati mai zuwa.
Gwamna El-Rufai ya faɗi haka ne a garin Gombe, a wajen kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnan jihar Yahaya Inuwa yayi.
Gwamna Inuwa ya gayyaci El-Rufai ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar take yi da wadanda ta kammala.
Sai dai kuma bayan haka da yake zantawa da manema labarai a garin Gombe, El-Rufai ya karyata rade-radin da ake yaɗawa wai yana neman a naɗa shi mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Tinubu idan aka rantsar da sabuwar gwamnati ranar 29 ga Mayu.
El-Rufai ya ce ” Ba mu taɓa zama ni da zaɓaɓɓen shugaban kasa mun yi irin wannan tattaunawa ba. Ni a ganina ba sai ka na cikin gwamnati ba ne za ka iya bada gudunmawar ka don cigaban kasa, ko daga can inda kake ma zaka iya bada gudummawar ka.
” Nan da kwanaki 22 bayan mun mika.mulki, hutu kawai make bukata ka’in da na’in. Sannan kuma mu maida hankali wajen bada kowacce irin gudunmawa da zamu bada don ci gaban kasa baki daya.
” Idan gudunmawa don ci gaba ake so, a kowani bangare kake zaka iya bada Irin taka, komai ƙanƙantanta kuwa.
A karshe El- Rufai yayi wa ƴan Najeriya albishir cewa Bola Tinubu ba zai ba maraɗa kunya ba, sannan kuma ba za ataɓa yin da na sani ba da zaɓen sa da aka yi, yan Najeriya za su yaba masa matuka.
Discussion about this post