Mahukunta a kasar Amurka sun bayyana cewa maharan da ake zargin ƴan kungiyar IPoB ne sun kai wa motocin ofishin jakadancin kasar a Najeriya a yayin wani tafiya na aiki da y kaisu jihar Anambra.
Bisa ga rahoton, Yan bindigan sun cinna wa motocin ma’aikatan wuta sannan kuma suka arce da wasu jami’an ƴan sanda biyu da wasu ma’aikata wanda duk ƴan Najeriya ne, baya ga wadanda suka arce da su cikin daji.
Mahuntan kasar Amurka sun ce ba bubu wani dan kasar Amurka da aka kashe ko aka sace a wannan hari sai dai suna tattaunawa da jami’an tsaron Najeriya don sanin ainihin abin da faru.
Duk da cewa babu kungiya da ta fito ta ce ita ce ta aikata wannan mummunar abu, ana zargin kungiyar IPOB, ma su fafutikar kafa kasar Biafra ne suka kai wannan hari.
Discussion about this post