Ni dai mace ce ‘yar yankin Arewa kuma mzauniyar yankin sai dai ba zan fadi jihar da na fito ba. Wani abu da yake ci mini tuwo a kwarya yanzu shine idan na duba yadda tarbiyya a yankin Arewa ya tabarbare, ya lalace ya sukurkunce gaba dayan sa. Abin yayi tsananin da babu budurwa babu matan aure.
A inda nake zaune na sha shiga tsakanin iyaye da ‘ya’yan su, matan aure da mazajen su domin in sasan tasa su. Wani abin da na yi ta karo da shi shine irin gudunmawar da iyaye ke bada wa wajen tabarbarewar tarbiyyar ‘ya’yan su ta hanyar nuna halin ko’in’kula da suke yi game da halinda suke ciki. Wani abin tashin hankali da tausayi da kuma ban mamaki shine yadda zaka ga tare da iyaye ake buga shedana ‘ya’ya na gani abau mai ce musu ci kanka ko kanki. Abin yayi munin da yakan koma kan iyayen daga baya idan ya’yan sun yi girma.
Za kaga uwa na gulama, tana zagin mahaifin ya’yan ta a gaban su, sannan kuma ta rika daure musu gindi suna shedanci a boye ba a sanar da mahaifin. Haka kuma za ka ga iyaye musamman mata na kallace kallacen fina-finai da basu da amfani tare da ‘ya’yan su ko kuma su kasance bisa waya na tsawon lokaci suna aikin banza ba karatun Kur’ani ba ko kuma wani abin da zai taimaka musu su kansu da ‘ya’yan su.
Uwa ta zama ita ce shedaniyar ba ‘ya ba. Duk abinda take yi shine ‘ya’yan su ke kwaikwayo. Sannan kuma su rika tunanin za girbi mai kyau. Hakan bazai taba yiwuba domin tarbiya ba ga tura da Islamiya bane kawai, har da abinda kake yi a a gaban da. Irin su kallace kallace banza a gaban yara. Za ki ga an taru a falo da uwa da ya’ya da abokanan uwa, da suaran yan gida duka ataru ana kallon fianfinan banza sannan kuma a sa ran wai da zai gyaru, ina ba zai taba gyaruwa ba domin ba a dauko hanyar dan ya gyaru ba.
Abin takaici ne kuma yadda abin sai dada tabarbarewa yake yi, mata sun afka cikin badala, sune shaye-shaye, madigo, zinace-zinace, rashin kunya, taurin kai, iskanci, kin zaman aure da fitina ta kowace hanya. Abin yayi munin gaske.
Sai kaga mace ta saka zumbulelen hijabi amma kuma badalar da take yi ya wuce nan. Yanzu har wani kwalliya mata ke yi na saka dankunne a hakora. Wasu na yi wa abin lakani da wani nau’i ne na nuna badala da kuma isa da kwarewa a rashin kunya. Kuma yanzu bai tsaya ga ‘yan mata ba kawai har da matan aure, yan bokon da ma dakikai. Dole fa a dawo a dage da addu’a domin abin ya tabarbare, ya lalace kuma kara gaba yake yi. Ba za ka ko ki san haka ba sai kin rika shiga manhajar TikTok, wasu matan zaka rantse fadawo suka yi daga sama ba su da iyaye saboda tsananin kwarewa wajen murza iskanci da rashin kunya.
Allah dai ya kara shirya mu da ‘ya’yan mu, Amin.
Discussion about this post