Alhassan Doguwa, ɗan majalisar tarayya wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa daga Jihar Kano, kuma wanda a yanzu haka ke fuskantar tuhumar zargin kisan ‘yan adawa a lokacin zaɓe, ya tsunduma neman kujerar Kakakin Majalisar Tarayya ta 10.
Doguwa ya bayyana shigar da cikin masu takara a cikin wasiƙar da ya aika wa dukkan zaɓaɓɓun ‘yan majalisar wakilai na ƙasa daban-daban.
A wasiƙar wadda ya aika masu ranar Lahadi, ya ce, “Ina so na yi amfani da wannan dama domin na isar maku da saƙo na cewa zan fito takarar Kakakin Majalisar Tarayya. Tsananin shauƙin da na ke da shi da tsantsar ƙaunar ganin na bayar da gudummawa wajen gina ƙasaitacciyar Najeriya ne ya sa na ke neman wannan ofis mai albarka, a wannan lokaci.”
Idan ba a manta ba, an tsare doguwa a kurkukun Kano, bayan an kama shi bisa zargin kashe wasu ‘yan jam’iyyar NNPP uku a mazaɓar sa, a lokacin zaɓe.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin kamun da ‘yan sanda su ka yi masa, inda su ka maka shi kotu a Kano, aka fara tuhumar sa da laifin haɗa baki a aikata kisan kai.
An kuma zarge shi da laifin haddasa ji wa wasu munanan raunuka, banka wuta da kuma tayar da hargitsi.
An dai bayar da belin sa a kan Naira miliyan 500.
A makon jiya ne kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kammala sauraren ƙarar da NNPPin Kano ta maka Alasan Doguwa, saura jiran yanke hukunci.
Kotun Ɗaukaka Ƙara a Kano ta kammala sauraren ƙarar da NNPP ta maka sake zaɓen Alhassan Doguwa, Ɗan Majalisar Tarayya na APC daga Kano.
Ɗan takarar NNPP Salisu Yusha’u ne da kuma NNPP su ka ɗaukaka ƙara zuwa kotun, inda alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ita George-Mbaba su ka amince cewa za su bayyana wa ɓangarorin biyu ranar da za su yanke hukunci nan gaba kaɗan. Daga nan kuma aka ɗage zaman sauraren.
A ranar 7 Ga Afrilu ne dai Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen ‘Yan Majalisar Tarayya da ‘Yan Majalisar Dokoki ta kori ƙarar da NNPP ta shigar, inda ta nemi kotun ta hana INEC gudanar da zaɓen da ba a kammala ba a wasu rumfunan zaɓen ƙananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a Jihar Kano.
Yusha’u da NNPP na neman Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin da Kotun Sauraren Shari’un Zaɓe ta yanke, wadda ta ce ba ta da hurumin hana INEC gudanar da zaɓen, kamar yadda masu ƙarar su ka nemi ta yi.
Yusha’u da NNPP har yau su na so Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jingine zaɓen 15 Ga Afrilu, wanda INEC ta ce Alhassan Doguwa ne ya yi nasara.
Lauyan wanda ake ƙara mai suna Idris Yakubu, ya gabatar wa kotu bayanan sa a ranar 25 ga Afrilu, inda ya nemi a kori ƙarar da Yusha’u da NNPP su ka shigar.
Alhassan Doguwa dai a yanzu haka ya na fuskantar tuhumar tayar da fitina a lokacin zaɓen farko wanda ake zargin sa da kisa da amfani da bindiga ba tare da lasisi ba.
Gidan Radiyon Freedom ya ruwaito Kwamishinan Shari’a na Kano ya ce ba su manta da waccan shari’a wadda aka bayar da belin Doguwa ba. Ya ce Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ne na Ƙasa da kan sa ya umarci a maida fayil ɗin binciken da ake wa Doguwa daga Kano, a maida shi Abuja.
Discussion about this post