Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta nesanta kan ta daga wani gungun mutanen da su ka ce wai sun goyi bayan tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Shugaban ACF na kudancin ƙasar nan ne ya bayyana cewa ACF ba ta cikin wata ƙungiyar da ta kira kan ta ‘Coalition ot Northern groups, wadda ta ce ta goyi bayan Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa.
Sa’idu ya yi wannan sanarwa ce a ranar Lahadi, a Abuja.
Ya ce shugabancin Akpabio ya Majalisar Dattawa zai zama wani bala’i ga Arewacin Najeriya.
“Mu na sanar da cewa ba mu cikin waɗanda ke goyon bayan Sanata Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa. Kuma babu ruwan mu da gungun masu kiran kan su ‘Coalition of Northern Group’, waɗanda su ka ce sun goyi bayan Akpabio
“Waɗannan gungun mutane dai ba da yawun Arewa su ka yi katoɓarar goyon bayan Akpabio ba.
“Babu cikakken ɗan Arewa mai kishin Arewa da zai goyi bayan Akpabio, saboda ba ya ƙaunar Arewa.
“Mu ne mu ka san Akpabio, kuma mu ka san ko shi wane ne. Saboda mu ne ke zaune a Kudu, mu mu ka san ‘yan Kudu masu kaunar Arewa. Kuma maganar gaskiya Akpabio ba ya cikin masu ƙaunar Arewa.”
Sa’idu ya ce ko dai waɗanda su ka ce sun goyi bayan Akpabio sun yi ne a bisa rashin sani, ko kuma kuɗi aka ba su kawai.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da Gwamna Ganduje na Kano ya ce gwamnonin APC sun ce Akpabio ne zaɓin su.
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bada sanarwar cewa gwamnonin jam’iyyyar APC sun yanke shawarar amincewa su zaɓi shugaban majalisar dattawa daga yankin Kudu maso Kudu.
Dama kuma a baya sun ce ko dai ya shugaban majalisar dattawa ɗin ya fito daga Kudu maso Gabas ko kuma ya fito daga Kudu maso Kudu.
Sun kuma yarda cewa muƙaman shugaban masu rinjaye da mataimakin masu rinjaye da kuma bulaliyar majalisa, a bayar da su ga ‘yan takarar da aka roƙa su ka janye.
Sai dai kuma a cikin wani bidiyo da aka datso daga gidan talabijin na AIT, an nuno Ganduje ya tabbatar da cewa gwamnonin APC sun amince a zaɓi tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, domin ɗan yankin Kudu maso Kudu ne.
A cikin bidiyon an nuno Ganduje tare da wasu gwamnoni ciki har da Ben Ayade na Kuros Riba a wurin taro da wasu mutane.
Ganduje ya ƙara tabbatar da cewa babu abin da zai canja tsarin raba muƙaman majalisar dattawa da na majalisar tarayya zuwa shiyya-shiyya, kamar yadda su gwamnonin su ka tsara.
“Shugaban Majalisar Dattawa mun yarda a bai wa ɗan Kudu maso Kudu. Kuma tsohon gwamnan Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio mu ke so a bai wa.” Inji Ganduje.
Discussion about this post