Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja ta bayuna cewa ta kama wani matashi mai shekara 16 bayan ya kashe mahaifinsa.
Kakakin rundunar Haruna Garba ya sanar da haka ranar Juma’a.
Garba ya ce matashin ya kashe mahaifinsa ne a ranar da ya ga Iyayen sa na dambe inda kawai cikin fushi sai ya dauki tabarya ya kwade mahaifinsa.
Ya ce wannan bugun da yaron ya yi ne ya yi ajalin mahaifinsa.
Garba ya ce rundunar za ta gurfanar da matashin a kotu 5da ake sauraren kararraki irin haka domin a gudanar da bincike akai.
Bayan haka kakakin rundunar ya ce fannin dake yaki da masu garkuwa da mutane ta ceto mutum 14 da akayi garkuwa da su inda a cikinsu akwai dagacen kauyen Chida dake gundumar Kwali a Abuja.
An yi garkuwa da wadannan mutane a ranar 7 ga Afrilu.
Ya ce mutum 10 daga cikin su sun kamu da rashin lafiya suna kwance a asibitin Abaji a na duba su.
Garba ya kara da cewa ‘yan sandan sun ceto wasu mutum 13 da aka yi garkuwa da su daga kauyukan Lapai da Tunga Mallam a jihar Niger ranar 13 ga Afrilu.
Ya ce za a damka wadannan mutane hannun Ardon Galadima dake karamar hukumar Lapai.