1. Ya samu bashin Nijeriya Naira Tiriliyan 12.2. Ya sauka ya bar bashin Naira Tiriliyan 77.
2. Kashi 90% na kuɗaɗen shigar Nijeriya a biyan bashi su ke tafiya.
3. Buhari ne Ministan Fetur, amma cikin shekara ɗaya an saci ɗanyen mai na Dala Biliyan 3.2.
4. Daga May 29, 2015 zuwa Octoba, 2022 jaridu sun buga labarin kashe mutum 58,000 da ɗoriya a kashe-kashe cikin faɗin ƙasar nan.
5. A ƙarƙashin mulkin Buhari Ma’aikatun Gwamnati sun ƙi maida Kasafin Kuɗaɗe wanda ba su kashe ba, har Naira Tiriliyan 5.2. An ƙwato Naira Biliyan 58 cikin watanni 18 da ƙyare, inji Zainab Ahmed, tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe.
6. Lokacin da Buhari ya hau, ya yi alƙawarin ƙwato kuɗin fetur Dala Biliyan 17 da aka sace tsakanin 2011 zuwa 2014. Amma ko sisi bai ƙwato a cikin kuɗin ba.
7. Tsadar rayuwa, fatara da talauci da tsadar abinci da masarufi sun hana a ga ƙoƙarin da Buhari ya yi wajen bunƙasa noma. Ya hau mulki buhun shinkafa ya na Naira 7,500. Ya sauka ya na N30,000, wani ma har Naira 50,000.
8. Cikin 2020 a mulkin sa, cutar daji (cancer), ta kashe mutum 78,000 da ɗoriya a Najeriya. Amma shiru ka ke ji, mutane ba su ma san hakan ta faru ba.
Babban Daraktan Cibiyar Kuda da Cutar Kansa ta Ƙasa ne ya bayyana haka, cikin watan Mayu.
9. Buhari ya ce zai gyara matatun fetur. Gyaran bai yiwu ba, amma a zamanin mulkin sa lokaci ɗaya an samu ƙananan matatun mai da ɓarayin ɗanyen mai su ke tace ɗanyen mai na sata a yankin Neja Delta.
10. Buhari ne shugaban da a zamanin sa ‘yan bindiga su ka buwayi jihar sa Katsina, har dubban ɗaruruwan Katsinawa su ka yi gudun hijira.
Sannan kuma ko shi ko shugabannin tsaron da ya yi aiki tare da su, babu wanda zai iya gane yawan ‘yan bindigar da ke cikin dazukan jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Neja da Kaduna, Arewar da ke tutiya da Buhari.
11. A zamanin mulkin Buhari ne talakawan cikin yankunan karkara da mutanen garuruwa da matafiya su ka fi tafka asarar kashe biliyoyin kuɗaɗe wajen biyan ‘yan bindiga kuɗaɗen fansar dangin su ko ‘ya’yan su ko iyayen su a hannun ‘yan bindiga, waɗanda ke cikin dazukan yankin Arewa maso Yamma, inda Buhari ya fito.
12. Ba a taɓa kama ɗan Najeriya ana yin garkuwa da su ba birjik kamar lokacin mulkin Buhari. Kuma ba a taɓa kama ɗalibai masu yawa ana garkuwa da su kamar zamanin mulkin Buhari.
Discussion about this post