Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta ƙara tabbatar da ɗaurin shekaru takwas kan tsohon shugaban Kwamitin Tsaftace Tsarin Fansho, Abdulrasheed Maina.
Kotun Tarayya ce ta same shi da laifin wawurar Naira biliyan 2 daga asusun ‘yan fansho.
Mai Shari’a Okon Abang ne ya ɗaure shi shekaru takwas a cikin Nuwamba, 2021 bayan an kama shi da laifuka 12 ɗin da EFCC ke tuhumar sa da aikatawa.
Da su ke jaddada hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa Maina, alƙalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara duk sun yarda da cewa an yi wa Maina adalci, saɓanin zargin da ya yi cewa ba a yi masa aldalcin jin ta ɓangaren sa sosai ba.
Ɗaya daga cikin Alƙalan, mai suna Elfreda Daudu-Williams, wanda shi ne ya karanto hukuncin na su, ya ce Maina ya kasa amfani da damar da kotu ta ba shi na ya kare kan sa.
“Ba a hana ka kare kan ka ba. Kuma ba a yi maka rashin adalci ba. Saboda Kotun Tarayya ta ba ka damar kare kan sa, amma ba ka yi amfani da damar ba.” Inji Mai Shari’a Daudu-Williams.
Ya ce hujjojin da Maina ya bayar a Babbar Kotun Tarayya ba su iya su gamsar da kotu cewa bai aikata laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa ba.
Dama kuma a cikin Nuwamba 2022 ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jaddada ɗaurin shekaru 14 da Babbar Kotun Tarayya ta yi wa ɗan Maina, Faisal Maina.
Discussion about this post