Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, shi da APC sun roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe kada ta amince da roƙon da Atiku, Obi da jam’iyyar APM su ka yi, na neman iznin su dunƙule ƙarar su wuri ɗaya, maimakon a riƙa sauraren kowane daban-daban.
Atiku da Obi da APM duk su na ƙalubalantar nasarar da INEC ta ce Tinubu ya yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Yayin da Atiku da Obi kowa ke neman ko dai a ba shi nasara, ko kuma a soke zaɓen a sake sabo, ita kuwa jam’iyyar APM ta shigar da ƙara cewa Tinubu bai ma cancanci tsayawa takara ba, don haka a soke zaɓen sa, a bai wa Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu nasara kawai.
Lauyan Tinubu mai suna Akin Olujinmi, wanda tsohon Antoni Janar na Tarayya ne, ya roƙi Alƙalai biyar masu shari’ar bisa jagorancin Haruna Tsammani cewa kada su bai wa su Atiku iznin dunƙule ƙararrakin na su wuri ɗaya. Ya ce idan aka yi haka, to an yi wa shari’a ita kan rashin adalci.
Duk da Olujinmi ya yarda cewa wasu ƙararrakin na su Atiku, Obi da APM iri ɗaya ne, ya ce ai kuma akwai inda su ka sha bamban.
A zaman da kotun ta yi na ranar Asabar dai, wannan jarida ta ruwaito cewa APC za ta gabatar da shaidu 25, Tinubu shaidu 39.
A ƙoƙarin ta na ganin Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP a zaɓen 2023 bai ƙwace nasara daga hannun Bola Tinubu ba, Jam’iyyar APC za ta gabatar wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa shaidu har guda 25.
A na sa ɓangaren, Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai gabatar da shaidu 39.
Babban Lauyan APC za shari’ar mai suna Solomon Jimoh shi ne ya bayyana wa kotun haka a ranar Asabar a zaman ta na ƙarshen mako. Ya ce zai gabatar da shaidu 25.
A ranar Litinin ce 22 ga Mayu za a ci gaba da zama, kamar yadda Shugaban Alƙalan Kotu su biyar, Haruna Tsammani ya yi sanarwa.
Atiku dai a ta bakin lauyan sa, ya shaida wa kotu cewa zai gabatar da shaidu 100, domin taya shi kai ƙeyar Asiwaju ƙasa.
Makonni biyu kafin a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu, a Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa kuma shari’a ta fara zafi yayin da aka kai matakin fara sauraren shaidun da za a fara gabatarwa a kotu.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, zai bijiro wa kotu da shaidu guda 100, domin ya tabbatar wa kotu zargin maguɗin da ya ke iƙirarin cewa an yi a zaɓen 25 ga Fabrairu, 2023.
A ɗaya ɓangaren kuwa, lauyoyin Tinubu sun bayyana wa kotu cewa za su gabatar da shaidu 39 domin kare zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da kujerar sa.
A ranar Asabar ce lauyoyin ɓangarorin biyu su ka gabatar wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa wannan aniya ko shiri da kowane ɓangaren ke yi.
Sauraren shari’un dai za su shiga surƙuƙin hayaƙi, bayan an shafe makonni biyu ana ban-tafin-hannun-makahon Turanci tsakanin lauyoyin a kotu.
Ana sa ran za a shafe watanni ana tafka shari’a har bayan rantsar da Tinubu kan mulki.
Ba za a kulle ƙofar shari’a ha har sai cikin Disamba, domin duk ɓangaren da bai gamsu da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa ba, ya na da damar wucewa Kotun Ƙoli.
Atiku ya na ƙalubalantar INEC cewa ba ta bi ƙaidojin da dokar ƙasa ta shimfiɗa ba kafin ta ayyana cewa Bola Tinubu ne ya yi nasara.
Haka shi ma Peter Obi na LP da ita jam’iyyar LP ɗin, sun shigar da kusan irin ƙara ɗaya da wadda Atiku da PDP su ka shigar.
A ranar Asabar, Babban Lauyan Atiku mai suna Chris Uche, ya bayyana adadin yawan shaidun da ɓangarorin lauyoyin biyu su ka amince za su gabatar wa kotu.
Sannan kuma sun amince da irin tsarin gabatar da kwafe-kwafen takardun hujjoji da za a riƙa gabatarwa.
“Mun yi shirin gabatar da shaidu har mutum 100. Za mu shafe makonni uku kaɗai mu na gabatar da shaidun mu ɗaya bayan ɗaya, maimakon makonni bakwai da aka ɗibar mana na ƙa’idar lokaci.” Inji Uche, babban lauyan Atiku.
“Ɓangarorin biyu sun amince cewa kowane mai shaida na mai ƙara da na mai kare kan sa, za a ba shi minti 30 ya yi magana a kotu.
“Sai lauyan wanda ake karewa kuma za a ba shi minti 15 ya yi masa tambayoyi. Sai kuma ƙarin minti biyar na ƙarƙare tambayoyin da ka iya biyo baya.”
Tinubu Zai Gabatar Da Shaidu 39:
Lauyan Tinubu mai suna Roland Otaru, ya shaida wa kotu cewa za su gabatar da shaidu 39 a matsayin shaidun kare nasarar Tinubu.
Otaru ya ce jagoran lauyoyin Tinubu, Wole Olanipekun zai buƙaci kwanaki 9 domin ya gabatar da shaidun na su.
“Sun kuma amince cewa ɓangaren da zai gabatar da kwafe-kwafen takardun shaida a kotu, zai aika wa ɗaya ɓangaren da kwafen su ma aƙalla sa’o’i 48 kafin zaman kotu.”
Sai dai lauyan Tinubu ya ce shaidun da za su riƙa gabatarwa kowane zai riƙa yin minti 20 ya na bayani a kotu, ba minti 30 kamar na shaidun Atiku ba.
Discussion about this post