Babban kotu dake Gwagwalada, Abuja ta raba auren shekara 15 dake tsakanin Okpanachi Yahaya da Zainab Adejoh saboda laifin cin amana a aure.
Alkalin kotun Abdullahi Abdulkareem a hukuncin da ya yanke ya umarci Zainab ta tabbatar ta kammala zaman iddan ta kafin ta yi wani auren.
Ya ce kotu za ta saurari karar da Yahaya ya shigar na neman ikon kula da ‘ya’yan su biyu masu shekara 14 da 12 a lokaci da daban da karar neman saki.
A kotun Yahaya ya bayyana cewa ya auri Zainab ranar 14 ga Satumba 2019 bisa ga sharuddan addinin musulunci.
Ya ce tun a shekarar ya fahimci cewa matarsa fa tana hulda da wasu mazajen.
Yahaya ya ce wata rana ya kama Zainab a dakin dafa abincin ta boye tana magana da wani saurayinta a waya inda bayan ya tambaye ta wanene ta haushi da balbalin bala’i.
” Daga nan kuma ta bini da duka saboda kawai na ne mi ko waye rake magana da shi.
Ya ce ya yi watanni hudu yana kwance a asibiti saboda rashin lafiya inda daga baya aka mai da shi kauye amma ko sau daya Zainab ba ta zo ta gan shi ba.
Yahaya ya ce tun da ya koma kauye da zama domin samun magani Zainab ke zuwa wurin aikin sa tana karbar albashinsa.
Ya ce a lokacin da yake kauye an bayyana masa cewa zinnan da matarsa ke yi ne ya sa yake fama da rashin lafiya.
“Manya sun shiga maganar domin ganin an sassanta mu amma Zainab ta ki.
“Babu sauran soyayya ko zaman aure tsakani na da Zainab sho yasa nake so a raba auren mu.
Ita ma Zainab din ta amince a raba auren haka nan.
Discussion about this post