Ƙungiyar Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Jihar Kano (ALGON), ta ƙaryata zargin cewa gwamnatin Jihar Kano na shirin kamfatar kuɗaɗen ƙananan hukumomin jihar, domin a sayi ƙuri’u da kuɗaɗen, a lokacin zaɓukan da ba su kammalu ba, wanda za’a yi a wasu yankuna da sassan ƙasar nan daban-daban.
Za a gudanar da zaɓukan ne a ranar 15 Ga Afrilu, 2023.
Zargin yin amfani da kuɗaɗen ya fito ne daga bakin Shugaban Kwamitin Karɓar Mulki na NNPP, Baffa Bichi.
Bichi ya yi iƙirarin cewa gwamnatin Kano na shirin kamfatar kuɗaɗen ƙananan hukimomin Kano 44, za a kashe su wajen sayen ƙuri’u a lokacin zaɓukan da za a ƙarasa ranar 15 Ga Afrilu.
“Saboda haka wannan kwamiti na jan hankalin dukkan shugabannin ƙananan hukumomi da sauran manyan jami’an kananan hukumomi cewa kada su bari a yi amfani da su a kwashe kuɗaɗen a sayi ƙuri’u da su. Kada su bari a karkatar da kuɗaɗen zuwa ga Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi.
“Mu na ba su shawara kada su bari a burma su cikin rami.” Inji Babba Bichi.
Sai dai kuma Shugaban ALGON na Kano, Baffa Muhammad ya ce zargin ba gaskiya ba ne, kuma ya shawarci NNPP ta bi a hankali kada ta ƙara ruruta siyasa a harkar aikin ƙananan hukumomi.
“Kada Kwamitin NNPP ya manta, akwai irin wannan zargin tun a cikin 2014, wanda ake zargin an kamfaci Naira miliyan 70 daga kowace ƙaramar hukuma 44 da mu ke da su, an kashe kuɗaɗen wajen kamfen ɗin takarar zaɓen fidda gwanin Rabi’u Kwankwaso a wancan lokacin. Yanzu haka maganar ta na gaban Hukumar Yaƙi da Rashawa.
A Kano dai za a yi zaɓuka a wurare 16 na ƙarashen zaɓen ‘yan takarar majalisar jiha, sai kuma ɗaya na Majalisar Tarayya mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa.