Mazauna yankin Ƙaramar Hukumar Gwadabawa cikin Jihar Sokoto na kwana su na tashi cikin zullumi da fargabar tsoron kai masu harin ramuwar-gayya, bayan sun kai hari wata rugar Fulani
Mutanen yankin sun fusata ne su ka yi gangamin kai wa gidajen Fulanin hari, bayan wasu da ake zargi Fulani ne ‘yan bindiga sun kai wa mutanen yankin mummunan harin da su ka kashe da dama.
Mazauna yankunan waɗanda akasari Hausawa ne, su kuma waɗanda ake zargin sun fara kai wa Hausawan hari, Fulani ne ake zargi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwadabawa, Aminu Aya, ya shaida wa gidan radiyon VOA Hausa cewa farkon rikicin ya samo asali ne tun da ‘yan bindiga su ka kai hari a ƙauyen Gigane har su ka yi garkuwa da mutane da dama.
Ya ce abin da masu garkuwa su ka aikata a Gigane ya harzuƙa jama’ar ƙauyen, har su ka yi gangami da wasu ƙauyukan da ke maƙautaka da su, inda su ka yi tattaki su ka afka wa Fulanin da ke yankin.
Ƙauyukan da aka bada labarin yin rikicin sun haɗa da Gigane, Shanyasu, Tungar Tudu da Sakamaru.
“An yi batakashi tsakanin sojojin Najeriya da ‘yan bindiga tsawon sa’a ɗaya, har aka rasa ran soja ɗaya, wani ɗaya kuma ya ji mummunan rauni.
“To dama akwai saɓani tsakanin Fulanin da mazauna ƙauyukan. An yi garkuwa da mutane da dama, su ma sai su ka kai wa Fulanin hari.”
Wani mazaunin yankin mai suna Zayyanu Sadiq, ya shaida wa VOA cewa maharan sun kashe har da dattijo mai shekaru da yawa, sannan kuma su ka bar saƙon cewa za su kai wa ƙauyen mummunan hari.
“To lokacin da su ka isa ƙauyen, sojoji na jiran su, saboda an kai masu rahoto. An yi kwarin wuta har aka kashe ‘yan bindigar da dama.
Sadiq ya ce shi ma an kashe kakan sa a wurin faɗan.
Aya wanda shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwadabawa, ya roƙi jami’an tsaro su ƙara himma sosai.
Discussion about this post