Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa zama mataimakin shugaban kasa da Kashin Shettima ya yi zai taimaka wajen rage masa nauyin shugabancin jihar Barno.
Zulum ya fadi haka a taron da aka shirya domin musayar ra’ayoyi tsakanin jigajigan jihar wanda ya samu halarcin zababben mataikin shugaban kasa.
Ya ce matsayin mataimakin Shugaban kasa da Shettima ya samu zai taimaka wajen raya jihar barno da kuma goge wa mutanen jihar hawaye bisa matsalolin da yake damun su.
“Daga yanzu zuwa shekaru hudu masu zuwa na samu danuwa na wanda zai rika taimaka mun wajen gina jihar mu.
Zulum ya yi kira ga mutanen jihar da su rika saka Shettima cikin addu’o’in su domin ganin ya zantar da aikinsa yadda ya kamata.
Discussion about this post