Ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi dai a makon da ya gabata ya fada hannun jami’an tsaron Landan, inda su ka tsare shi, bisa laifin yin sojan-gona.
Kakakin Yaɗa Labaran Obi-Datti mai suna Diran Onifade ne ya sanar da haka a ranar Laraba.
Sai dai kuma ya ce an sako Peter Obi, har ma ya dawo gida Najeriya.
“Peter Obi ya isa filin jirgin Heathrow da ke Landan a ranar 7 Ga Afrilu, 2023, daga nan ya shiga layin duba masu shiga ƙasar Ingila. Ya na kan layi ne wasu jami’an shige-da-fice su ka same shi, su ka damƙa masa sammacin sanar da shi za a tsare shi. Kuma aka umarce shi da ya fito daga layi, ya miƙa kan sa wurin jami’an tsaro.”
Sanarwar ta ce an ci mutuncin Peter Obi, sannan aka garƙame shi, inda ya shafe kwanakin Easter a tsare.
“An tsare shi ana yi masa tambayoyi, kai ka ce kamar bai taɓa shafe shekara 10 a Ingila ba.” Inji sanarwar Onipade.