Kotun Ɗaukaka Ƙara a Kano ta kammala sauraren ƙarar da NNPP ta maka sake zaɓen Alhassan Doguwa, Ɗan Majalisar Tarayya na APC daga Kano.
Ɗan takarar NNPP Salisu Yusha’u ne da kuma NNPP su ka ɗaukaka ƙara zuwa kotun, inda alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ita George-Mbaba su ka amince cewa za su bayyana wa ɓangarorin biyu ranar da za su yanke hukunci nan gaba kaɗan. Daga nan kuma aka ɗage zaman sauraren.
A ranar 7 Ga Afrilu ne dai Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen ‘Yan Majalisar Tarayya da ‘Yan Majalisar Dokoki ta kori ƙarar da NNPP ta shigar, inda ta nemi kotun ta hana INEC gudanar da zaɓen da ba a kammala ba a wasu rumfunan zaɓen ƙananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a Jihar Kano.
Yusha’u da NNPP na neman Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin da Kotun Sauraren Shari’un Zaɓe ta yanke, wadda ta ce ba ta da hurumin hana INEC gudanar da zaɓen, kamar yadda masu ƙarar su ka nemi ta yi.
Yusha’u da NNPP har yau su na so Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jingine zaɓen 15 Ga Afrilu, wanda INEC ta ce Alhassan Doguwa ne ya yi nasara.
Lauyan wanda ake ƙara mai suna Idris Yakubu, ya gabatar wa kotu bayanan sa a ranar 25 ga Afrilu, inda ya nemi a kori ƙarar da Yusha’u da NNPP su ka shigar.
Alhassan Doguwa dai a yanzu haka ya na fuskantar tuhumar tayar da fitina a lokacin zaɓen farko wanda ake zargin sa da kisa da amfani da bindiga ba tare da lasisi ba.
Gidan Radiyon Freedom ya ruwaito Kwamishinan Shari’a na Kano ya ce ba su manta da waccan shari’a wadda aka bayar da belin Doguwa ba. Ya ce Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ne na Ƙasa da kan sa ya umarci a maida fayil ɗin binciken da ake wa Doguwa daga Kano, a maida shi Abuja.