Daga cikin sauran ɗalibai mata 11 da ke hannun gogarman ɗan bindiga Dogo Giɗe, wanda ya sace ɗalibai sama 100 a cikin 2021, cikin wannan makon an sako 4, yanzu saura 7 kenan a hannun tantirin ɗan bindigar.
Dogo Giɗe ya sako ɗaliban mata su 4 bayan an biya kuɗin fansa har naira miliyan 80, tare da shafe kwanaki shida ana tattauna yadda za a sako su tsakanin ɗan bindigar da iyayen yaran.
Ɗalibai huɗun da aka sako su ne Bilha Musa, Faiza Ahmed, Rahma Abdullahi da Hafsa Murtala.
PREMIUM TIMES ta ji daga bakin ɗaya daga cikin iyayen yaran da aka sako ɗin cewa Dogo Giɗe ya sake su bayan an biya shi fansar naira miliyan 80.
Ya ce an sake su a ranar Juma’a, ƙarfe 8:37, kamar yadda wanda ya ke shugaban ƙungiyar iyayen ɗaliban da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Tarayya ta Yauri ya shaida wa wakilin mu.
Ɗaliban mata su huɗu dai ko da aka bayar da su, sai Giɗe ya sa yaran sa uku su ka ɗauke su kan babura, su ka kai su wani ƙauye wajen Ƙaramar Hukumar Koko a Jihar Kebbi. Daga can ne kuma masu jiran su karɓi yaran su ka karɓe su zuwa Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Giɗe da yaran sa sun yi garkuwa da ɗaliban cikin Yuni, 2021 a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri a Jihar Kebbi, inda su ka kwashi ɗalibai sama da 100.
Daga baya sun riƙa sako su, amma a ƙarshe su ka riƙe mata 11. Da yawa an sako su bayan an riƙa biyan diyya, wasu kuma an sako su bayan gwamnati ta saki wasu yaran Dogo Giɗe da aka kama.
Ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban mai suna Sani Mohammed, ya shaida wa wakilin mu cewa an biya fansar naira miliyan 80 kafin Dogo Giɗe ya saki ɗaliban 4.
Ya ce Giɗe ne da kan sa ya zaɓi waɗanda zai saki daga cikin matan 11 da ke hannun sa. Yanzu bakwai kenan su ka rage ba a kai ga saki ba.
“A maganar ƙarshe da mu ka yi da shi, ya yi alƙawarin idan aka cika masa kuɗin da ya ke nema a biya shi, to zai saki sauran.
“Har yanzu bai saki ɗiya ta ba. Amma dai mu na sa rai cewa nan ba da daɗewa ba zai sake ta,” inji Sani.
Sani wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya yi ritaya, ya shaida wa wakilin mu cewa sun shafe kwanaki shida su na tattaunawa da ‘yan bindiga kafin su amince su saurare su.
“Ka san da farko cewa ya yi naira miliyan 100 ya ke so a biya shi. To dai wata rana sai ya kira ni, na shaida masa gaskiyar halin da ake ciki na tsananin rayuwa. Sai ya ce zai iya rage naira miliyan 20. Don haka a biya naira miliyan 80 kenan,” inji Sani.
Wakilin mu ya ji cewa wani Abubakar mai shiga tsakanin iyayen da kuma su Dogo Giɗe. Iyayen da kuma Dogo Giɗe duk sun amince da gaskiyar Abubakar. Kafin Abubakar dai sau uku ana canja mai shiga tsakani, saboda rashin amincewa a tsakanin su.
Salim Kaoje wanda shi ne shugaban iyayen yaran da ke hannun su Giɗe, ya tabbatar wa wakilin mu cewa mai shiga tsakanin da wasu iyayen yaran su biyu su na cikin daji, su na roƙon Giɗe ya taimaka ya saki sauran yaran bakwai da ke hannun sa.
“Waɗanda Ya saki su huɗu mu ne mu ka sayar da kadarorin mu, mu ka haɗa kuɗaɗen, sai kuma gudummawar da jama’ar da ke tausaya mana su ka riƙa bayarwa. Amma babu ko sisi na gwamnati,” inji shi.
Kaoje ya ce har yanzu akwai ƙanuwar sa Farida a hannun Giɗe, a cikin waɗanda ba a sako ba.
Ya ce an yi tsammanin gaba ɗaya Giɗe zai saki, amma sai ya saki huɗu ya riƙe bakwai. “Wannan shi ne dalilin da ya sa mai shiga tsakani da iyayen biyu har yanzu su ke cikin daji, su na roƙon sa ya saki sauran ɗalibai bakwai da ke hannun sa.”
Labari Mai Ban-takaici: Yadda Gogarma Dogo Giɗe Ya ‘Auri’ ‘Ya Ta Farida Wacce Ya Kama A Kwalejin Yauri, Cikin 2021 -Sani Yauri, Mahaifin Farida:
Masu karatu su fahimci cewa PREMIUM TIMES Hausa ta buga wannan labari mai ban-tausayi da takaici tun cikin watan Satumba, 2022:
Cikin wata tattaunawa da mai ban-tausayi, cike da damuwa ƙuncin rayuwa, Sani Giɗe ya shaida wa wakilin mu yadda a halin ‘yanzu ‘yar sa Farida Sani ke hannun gogarman ‘yan bindiga Dogo Giɗe, a matsayin amaryar sa da ya yi wa auren-dole, bayan sun kai hari a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri, ranar 17 Ga Yuni, 2021.
Idan ba a manta ba, a farmakin dai an kwashi ɗalibai 90 da kuma malamai. Amma an riƙa ceto wasu, daga baya kuma an riƙa tattaunawa da Gwamnatin Jihar Kebbi ana sakin wasu da kaɗan-kaɗan.
Zuwa cikin watan Janairu lokacin da aka saki ƙarin ɗalibai 30, saura ‘yan mata 11 ne su ka rage wurin su Dogo Giɗe, waɗanda ya tabbatar da cewa sun raba su a tsakanin su ‘yan bindigar, sun aurad da su, saboda Gwamnati ta ƙi biyan su kuɗin fansar da su ka nemi a biya su.
Sani Kaoje shi ne mahaifin ɗaya daga cikin ɗalibai mata da su Gogarma Dogo Giɗe su ka aura. Ya shaida wa PREMIUM TIMES irin yadda ya riƙa waya da Dogo Giɗe sau tarin yawa dangane da ‘yar sa da har yanzu ke hannun sa, a matsayin amaryar sa.
“Ina da ‘ya’ya 19 kuma mata na uku. Farida ita ce ta 15, kuma yanzu shekarun ta 16. Wato kenan ta na da shekaru 15 aka yi garkuwa da ita” Inji Sani Kaoje.
Ya shaida cewa sau da yawa Dogo Giɗe na kiran sa ya na nuna masa cewa tun da ba za a biya su naira miliyan da babura 30 da su ka nema ba, to za su auri yaran.
“Na sha yin waya da shi. Saboda ya na kira na sosai. Har dai ta kai ya nuna min cewa sun auri yaran. Bai fito ya nuna min cewa shi ya auri Farida ‘ya ta mai shekaru 15 a lokacin da aka kama ta ba. Amma sai ya karkatar da maganar ya ce min ta na hannun sa, shi ke kula da ita. Amma daga ƙarshe ya ce min matar sa ce, kuma ko ya mutu, a cikin gidan su akwai wanda zai gaje ta.”
Kaoje ya ce tabbas ya na yin waya da ‘yar sa Farida ba sau ɗaya ko sau biyu ba. Amma dai Dogo Giɗe ɗin ne ke kiran sa a waya, sai ya haɗa su su gaisa.
“Akwai ranar da ya haɗa da ita mu ka yi waya, ta kira ni ta ce min Baba akwai fa matsala, saboda za su aurad da mu.” Ni kuma dama ya rigaya ya shaida min haka.
Sani Yauri ya nuna gazawar Ministan Harkokin Ilmi Adamu Adamu, wanda ya ce bai yi komai ba, duk kuwa da cewa makarantar da aka sace yaran ta Gwamnatin Tarayya ce.
Sannan kuma ya shaida wa wakilin mu cewa Dogo Giɗe ya ce shi Gwamnati ya ke so ta sasanta da su, ba iyayen yaran ba.
“Dogo Giɗe ya ce min tun su na neman a biya su fansar naira miliyan 100, su ka rage su ka ce a biya naira miliyan 50 da babura 30, amma gwamnati ta yi banza da su. Wai shi ya sa su ka yanke shawarar aurar da sauran ‘yan matan da su ka rage a hannun su.” Inji Sani Yauri, wanda tsohon ma’aikacin gwamnati ne daya yi ritaya.
A ƙarshe ya nuna irin halin ƙuncin da su ke ciki, tun daga ranar da aka yi garkuwa da ‘ya’yan su har yau ɗin nan.
“Wasu iyayen sun mutu saboda takaici. Akwai kuma mahaifin wata ƙawar ‘ya ta mai suna Rebecca. To mahaifin ta ya shiga damuwar da ba ya iya hasala komai a rayuwa. Ko kuɗi ka miƙa masa, ba zai iya ƙidaya su ba.”
Discussion about this post