‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 80 a kauyukan dake karamar hukumar Tsafe jihar Zamfara ranar Juma’a da safe.
Mazaunan karamar hukumar da suka tattauna da ƴan jarida sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun sace mutanen da suka fita yin ice da sanyin safiyar ranar Juma’a wajen misalin karfe 7 na safe a dajin dake gefen gari.
Wasu kuwa sun je yin shara gonakinsu gabanin faduwar damina.
Wani basarake da baya so a fadi sunnan sa ya ce “ Muna zaune da misalin karfe 8 na safe sai muka ji ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matasan da suka shiga daji samo itace.
Barasaken ya ce mutanen da maharan suka tafi da su za su kai mutum 80 zuwa 100.
“Ba zamu iya fadin yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ba amma muna tsammanin mutanen da maharan suka sace za su kai 80 zuwa 100 sannan Mafi yawan su matasa ne da basu wucewa shekara 20 ba duk da cewa akwai wasu tsofaffi masu shekaru 50.
Ya ce daga daga cikin mutanen da suka shiga dajin ya ji rauni a jikinsa inda a yanzu haka yana asibiti likitoci na duba shi.
“Wasu da dama daga cikin yawan da maharan suka tafi da su sun kubuta sannan har sun dawo gida.
Discussion about this post