Akalla mutum 8 ne ‘yan bindiga suka kashe a Wani harin da suka kai a karamar hukumar Zangon Kataf jihar Kaduna.
Shugaban kungiyar Atiyap Sam Timbuwak ya sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis.
Timbuwak ya ce maharan sun afka musu da misalin karfe 9 na safiyar Laraba.
Ya ce maharan sun shigo karamar hukumar daga wani daji dake kusa da wurin inda suka shigo suna harbi ta ko Ina har suka kashe mutum 8.
Timbuwak ya ce sun kona gidaje 5 kuma wasu mutum 4 sun ji rauni.
Ya ce jami’an tsaro sun kawo dauki bayan maharan sun gama duk abinda za su sun arce cikin daji.
Timbuwak ya koka da rashin zuwan jami’an tsaron da wuri tana mai cewa hakan ya sa mahara suka ci karen su babu babbaka a lokacin da suka kawo hari garin.
Ya yi kira a gare su da su zage damtse wajen gudanar da aikin su musamman wajen kamo mutanen da suke yawan kai wa karamar hukumar hari.
Bayan haka Timbuwak ya ce mahara sun kai wa kauyen Langdon hari inda suka kashe mutum 10 a kauyen.
Zuwa lokacin da aka rubuta labarin kwamishinan tsaro na jihar Samuel Aruwan da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammed Jalige duk ba su ce komai game da harin ba.