Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana yadda ya sha fama kafin ya samu gidan haya, cikin 1989 da ya yi aure, a Legas.
“Lokacin da ranar bukin aure na ya gabato a 1989, na shiga fagamniya da gaganiyar neman gidan haya. Na samu wani lauya wanda shi ya fi maida hankali wajen yin ejan ɗin bayar da haya, maimakon shiga kotu.
“Da na samu ejan ɗin gidajen nan, wanda dattijo ne, ya ce min tabbas akwai irin gidan da ka ke buƙata, kuma daidai ƙarfin ka. Sai dai kuma ni a gaskiya ba na bai wa wasu mutane uku hayar gida: Ba na bai wa ɗan ƙabilar Igbo, ba na bai wa Bayaraben Ijebu, sannan kuma ba na bai wa lauyoyi haya.”
Osinbajo ya bayyana irin yadda mutumin ya tsani ko kuma ya tsananta nuna wa Yarabawan jinsin Ijebu ƙabilanci.
Osinbajo wanda Babban Lauya ne (SAN), ya shiga mawuyacin hali sosai da ya kasa samun gidan hayar, saboda ƙabilancin da ejan ɗin ya nuna masa don ya na Bayarabe, amma a cikin Yarabawan ma, jinsin Ijebu.
Osinbajo ya bada wannan labarin abin da ya shafe shi a wurin taron Sanin Nagartar Aiki, a Makarantar Horon Kwarewar Mulki da Nagartar Aiki, NIPSS.
“Haka dai ejan ɗin nan kuma lauya ya wulaƙanta ni. Ya nuna min wasu tarkacen litattafai da ke kan kantar ofishin sa, ya ce min da waɗannan littafai na ragargajar duk ɗan hayar da ya nemi wahalar da ni idan mun je kotu.
“Sai daga baya kunya ta kama shi, yayin da ya gano ashe ni malamin koyar da aikin lauya ɗin ne ma sukutum, kuma ɗan ƙabilar Yarabawan Ijebu da ya tsana. Sannan kuma Mashawarcin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya.”
Osinbajo ya buga wannan misali ne a cewar sa, ganin yadda aka yi amfani da ƙiyayya da ƙabilanci a zaɓen 2023, inda ya ce a wasu wuraren abin takaici, har cin zarafin mutane an riƙa yi, ana hana su yin zaɓe, saboda ƙabilanci.
Discussion about this post