Shin akwai bukatar dogon sharhi ne a kan irin azabar da muke sha na tsananin zafi a irin wannan lokaci?
Sanin kowa ne, lalacin mu ne da kuma rikon sakainar kashin da muka yiwa muhallin mu ne, yasa muka gaza yiwa kanmu maganin irin wannan yanayin.
Duniya tayi mana karatu, zamani yayi mana gargadi da abin da Bature yake kira Climate Change da kuma Global Warming, amma ko a jikin mu.
Malamai sun yi mana wa’azi akan falalar shukawa da rainar bishiya, amma mun gaza maida hankali don samun wannan ladan.
Wani a bin takaici, koma a bin dariya, shine yadda mutane cikin Azumi suna yawo neman inuwar da zasu tsugunna, wani lokacin sai an kai ga zuwa bakim kududdufi ko kogi don samun sa’idar sanyi, amma mun gaza yin dogon tunanin samun mafita don inganta muhallan mu.
Zamu iya inganta muhalan my ta wajen shukawa da dasa bishiyoyi, ita ce hanya mafi sauki, amma yin hakan ya zama abu mai wahala.
Shuka bishiya da yiwa muhalli gata, yafi karfin gwamnati ita kadai, dole sai mu mutane mun shiga munyi aiki tukuru.
Shuka bishiya ba shine wahala ba, amma renon bishiyar har ta girma shine ke zama kalubale gare mu.
Amma in muka kudiri aniya, muka yi aiki tukuru, zamu iya kawo chanjin a muhallan mu.
Mu dasa bishiya, mu ceto muhallan mu.
Discussion about this post