Babban kotu dake Ikeja jihar Legas a ranar Laraba ta yanke wa wani kafinta mai shekaru ,32 Onyekachi Agu, hukunci zama a kurkuku na tsawon shekara 7 dalilin kwarara wa tsohuwar budurwarsa Aishat Adefarati da sabon saurayinta ruwan batir.
Alkalin kotun Oyindamola Ogala ya ce Agu bai iya gabatar da dan uwansa wanda suke tare a wannan rana da lokacin da suka ziyarci Aisha da saurayinta Ahmed.
“Sannan kwarara wa Aisha da Ahmed ruwan batir da Agu ya yi ya nuna cewa da gangar ya aikata hakan.
Aisha da Ahmed sun gabatar da hotunan raunin da suka ji a dalilin ruwan batir din da Agu ya kwarara musu a kotu.
Alkalin ya ce bayanan da Aisha ta yi ya nuna yadda Agu ke cin zarafin ta tun a lokacin da suke tare dalilin da ya kawo rabuwarsu bayan sun yi shekara uku sun amurza soyayya.
“A dalilin hujoji da bayanan da kotu ta samu ya sa kotun ta yanke wa Agu hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekaru 7.
Agu ya nemi afuwar Ahmed da kotun da su yafe masa.
Fannin da suka shigar da kara sun bayyana cewa Agu ya aikata haka ne ranar 3 ga Yulin 2020 a otel din dake Gangare Mile 12 a Legas.
“A wannan rana Agu ya kwarara wa tsohuwar budurwarsa da sabon saurayinta ruwan batir bayan ya binciki wurin da suka shan iska.
Discussion about this post