Zababben Shugaban kasa Bola Tinubu da uwargidansa Oluremi sun rabawa Musulmai da Kiristoci 100,000 kayan abinci a Abuja.
Shugaban mata na jami’iyyar APC Betta Edu ce ta raba kayan a madadin Tinubu da uwargidansa.
Yayin da take rabon kayan abincin a babban masallacin Abuja Edu ta ce an raba abincin ne domin tallafa wa mutane a Lokacin azumin Ramadan da kuma domin bikin Easter.
Ta ce raba abincin zai taimaka wajen karkato da hankalin mutane wajen son junansu, inganta zaman lafiya tare da yi wa kasan addu’o’I musamman a wannan lokaci.
Edu ta yi kira ga Kiristocin kasar nan su rika yi wa kasar nan addu’a domin samun zaman lafiya, tsaro, hadin kan mutane da albarka.
“Zababben Shugaban kasa tare da uwar gidan sa sun umurce mu da mu raba wa Musulmai kayan abinci a wannan wata na Ramadan wanda lokaci ne na nuna kauna da yi wa mutane kyauta.
“Za a raba abu mai kamar haka ga Kiristocin dake Abuja suma kayan abinci domin tallafa musu dominsamun yalwa a hidimomin Easter.
“Muna kira ga ‘yan Najeriya da su rika yi wa kasar nan addu’a saboda kasar nan namu ne duka Kuma kowa na da rawar da zai iya takawa wajen gina kasar.
Edu ta yi kira ga duk ‘yan Najeriya da su mara wa Tinubu da mataimakinsa baya domin tana da tabbacin cewa za su kawo ci gaba a kasar masu ma’ana.