A ranar Laraba ce Gwamnatin Najeriya ta fara kwaso ‘yan ƙasar ta, waɗanda yaƙi ya ritsa da su a Sudan.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wata sanarwar da Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta wallafa a shafin ta na Tiwita.
NiDCOM ta nuno motoci sun yi layi ga kuma mutane akasari ɗalibai su na shiga motocin.
“Jiya da dare tawagar ceto ‘yan Najeriya daga Sudan ta samu wasu motoci ƙirar bas sun fara kwasar ‘yan Najeriya ɗalibai da ke Sudan. Ana kwasar su ne zuwa kan iyakar Masar, kafin jirgi ya kwaso su zuwa Najeriya. Gwamnatin Najeriya ce ta samar da wannan mafiya ta hannun hukumar NEMA da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Sudan,” inji NiDCOM.
NiDCOM ta ce wasu motoci masu yawa za su je a yau Laraba su ci gaba da kwaso sauran ɗaliban.
An kashe mutum sama da 500 tun bayan fara yaƙin Sudan a makon da ya gabata. An kuma tabbatar da fiye da mutum 4,100 su ka ji raunuka.
Ƙasashe da dama ciki har da Birtaniya, Saudi Arabiya, Ukraine da Faransa duk sun kwashe mutanen su daga Sudan.
Sau huɗu ana ƙoƙarin ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin makon jiya, amma abin ya ci tura.
Sai dai kuma a yanzu Amirka ta yi nasarar ƙulla yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu masu yaƙi da juna.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, sun amince su tsagaita wuta tsawon kwanaki uku, domin a bai wa ƙasashe damar kwaso ‘yan ƙasar su, su ma ‘yan Sudan su samu damar guduwa wurin da za su ɓuya.
Discussion about this post