Hedikwatar tsaron Najeriya, DHQ ta bayyana cewa sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 54, an ceto mutum 468 a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a cikin makonni biyu da suka wuce.
Darektan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron manjo-janar Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce a tsakanin wannan lokacin dakarun sun kama ‘Yan ta’adda da ‘yan bindiga 122 a wadannan wurare.
Danmadami ya ce daga cikin mutum 468 din da suka ceto akwai mutum 30 da suka ji rauni suna asibiti likitoci na duba su yayin da aka hada saurarn da ‘yan uwansu.
A yankin Arewa maso Gabas rundunar ‘Operation Hadin Kai sun kashe Boko Haram/ISWAP 24 sannan sun kama mutum 40 da ke hada baki da maharan tare da ceto mutum 206 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce Boko Haram/ISWAP da iyalen su 501 sun mika wuya da a cikinsu akwai maza 60, mata 176 da yara 266.
“ Dakarun sun kama manyan bindigogi kirar AK-47 14, bindiga kirar AK-49 biyu, bindiga kiran AK-56 daya, bindiga kirar GPMG daya, bindiga kirar RPG daya, bindiga kirar PK MG daya da bamabamai.
Sannan an kama tulin harsasai da bindiga kirar hannu da kudi Naira 103,505.
A Arewa ta Tsakiya rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ‘Operation Whirl Stoke’ sun kama bata gari mutum 44 sannan sun ceto mutum 252.
Ya ce dakarun sun kwace wayoyin salula 18, masu sata a layin dogo mutum 38 da dai sauran su.
A Arewa ta Yamma Danmadami ya ce ‘Operation Hadarin Daji’ sun kashe ‘yan bindiga 30, sun kama wasu guda 33 sannan sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su.