Wasu mambobin Majalisar Wakilai ta Tarayya sun ƙaryata zargi da raɗe-raɗin da Gwamnonin APC su ka yi, inda su ka ce akwai wasu masu ƙoƙarin sayen kowace ƙuri’ar neman Shugaban Majalisar Dattawa da ta Kakakin Majalisar Tarayya ɗaya kan Naira miliyan ɗaya kowace.
Akin Alabi ɗan APC daga Oyo da Rolland Igbakpa, ɗan PDP daga Delta duk sun ƙaryata gwamnonin APC, sun ce zargin su ba gaskiya ba ce.
Su biyun sun ce babu mai irin waɗannan mahaukatan kuɗaɗe kakaf a cikin majalisa baki ɗaya.
Sun bayyana haka ne a ranar Laraba, a inda aka tattauna da su a shafin Tiwita na PREMIUM TIMES.
Su biyun sun ce babu wanda ya tunkare ya yi masu tayin waɗannan mahaukatan kuɗaɗe. Kuma ba a tunkari kowa ba.
Sun tunatar cewa a 2019 babu wani ɗan majalisar da aka bai wa kuɗaɗe don ya zaɓi Femi Gbajabiamila. “Maimakon haka ma, mu ne mu ka riƙa kashe kuɗaɗen aljihun mu a wajen ɗaukar ɗawainiyar jeƙala-jeƙalar neman a zaɓi Gbajabiamila. Kuma a haka ya samu sama da ƙuri’u 200.”
Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa, ana raɗe-raɗin mutum biyu masu takarar shugabannin Majalisar Dattawa da ta Tarayya sun fara taya kowace ƙuri’a ɗaya dala miliyan ɗaya.
A cikin labarin dai ana zargi da raɗe-raɗin cewa wasu ‘yan Majalisar Dattawa da Wakilai ta Ƙasa su biyu, sun dulmiya cikin ƙazamin sayen ƙuri’un mambobin su domin buƙatar su ta zama shugabannin majalisa ya tabbata.
Su biyun dai duk da ba a bayyana sunayen su ba, an tabbatar cewa duk ‘yan Jam’iyyar APC ne.
Su biyu waɗanda ɗaya na neman zama na uku a ƙarfin mulki, wato Shugaban Majalisar Dattawa da kuma ɗayan mai neman zama na huɗu, wato Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, sun shirya tsaf domin bai wa sauran ‘yan majalisa rashawar dala miliyan 1 kowanen su domin su jefa masu ƙuri’a.
Gwamnonin da zaɓa a ƙarƙashin APC ne su ka fallasa wannan gagarimar badaƙala, a cikin wata wasiƙar da su ka aika wa Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Gwamnonin APC sun shaida wa Tinubu cewa ‘yan majalisar su biyu sun tabbatar da aniyar su ta sayen ƙuri’ar kowane ɗan majalisa daga dala 500,000 zuwa dala miliyan 1.
“Mu na jin tsoron kada fa a kai ga maimaita abin da ya faru a 2015, ganin yadda ake ta zawarcin ‘yan majalisar jam’iyyun adawa.”
Wannan jarida ta ruwaito cewa Gwamnonin APC sun rubuta wa Tinubu wasiƙa dangane da batun tsarin karɓa-karɓa shugabancin Majalisar Dattawa da ta Tarayya.
Sun rubuta wa Tinubu wasiƙa bayan sun tashi daga wani taro a ranar 8 Ga Afrilu, inda su ka sanar da shi cewa waɗanda su ka ware maƙudan kuɗaɗen don su kashe wajen cuwa-cuwar sayen ƙuri’u daga sauran sanatoci da bambobi, za su yi amfani da kuɗi ne ta yadda za su tarwatsa tsarin karɓa-karɓa.
Sun ce masu takarar har sun fara zawarcin sabbin-shigowar majalisa da dubunnan daloli domin su saye su a ranar zaɓen shugabannin majalisun biyu.