Wasu mambobin Majalisar Wakilai ta Tarayya sun soki tsarin karɓa-karɓar da Gwamnonin APC ke so a bi wajen zaɓen Shugabannin Majalisar Dattawa da na Tarayya Zango na 10.
A wata tattaunawa da aka yi da Akin Alabi, ɗan APC daga Oyo da kuma Rolland Igbakpa, ɗan PDP daga Delta, sun ce zai yi wahalar gaske bayar da manyan muƙaman majalisar dattawa da ta tarayya ga yankunan Arewa, bisa la’akari da cewa Bola Tinubu da Kashim Shettima sun ci zaɓe a ƙarƙashin tikitin Muslim-Muslim.
Da ake tattaunawa da su a shafin Tiwita ɗin PREMIUM TIMES dangane da yadda Majalisar Tarayya Zango na 10 Za Ta Kasance, sun ce amma dai maganar gaskiya idan aka dubi yadda aka yi Muslim-Muslim a APC, kuma sannan aka yi la’akari da wasu batutuwa na siyasa, to maganar a bayar da masu manyan muƙamai ga Arewa bai ma taso ba.
Yadda Gwamnonin APC Ke So A Raba Muƙaman Shugabancin Majalisar Dattawa Da Ta Tarayya:
Cikakken bayanin yadda za a bi tsarin karɓa-karɓa a zaɓi shugabannin Majalisar Dattawa da na Tarayya:
Ƙungiyar Gwamnonin APC sun rubuta wa Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu wasiƙar roƙon ya gaggauta shiga tsakani ta yadda za a zaɓi shugabannin Majalisar Dattawa da shugabannin Majalisar Tarayya, wato Majalisar Wakilai ta Ƙasa a bisa tsarin karɓa-karɓa.
Sun rubuta takardar ce tare da nuna damuwar cewa akwai buƙatar a samu daidaiton raba-daidai bisa adalci a shugabancin majalisun biyu, domin akwai wasu ‘yan takarar da su ka nuna maitar su a fili, har su ke ƙoƙarin sayen kowace ƙuri’ar ɗan majalisa ɗaya kan dala 500,000 zuwa dala miliyan 1.
Karɓa-karɓa: Yadda Gwamnonin APC Su Ka Tsara Rabon Muƙaman Shugabannin Majalisar Dattawa Da Ta Wakilan Tarayya:
1. Ya kamata a bai wa Kudu maso Gabas ko Kudu maso Kudu Shugaban Majalisar Dattawa.
2. Shugaban Majalisar Dattawa ya kasance Kirista ne daga Kudu maso Kudu, ko Kudu maso Gabas, ko kuma Arewa Ta Tsakiya (North Central).
3. Ya kamata Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya ya fito daga Arewa maso Yamma, ko Arewa ta Tsakiya (North Central).
4. Muƙaman Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakin Masu Rinjaye a bayar ga ‘yan takarar da su ka janye a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Tarayya.
5. Muƙamin Bulaliyar Majalisar Dattawa da Bulaliyar Majalisar Wakilai ta Tarayya a bayar ga ‘yan takarar neman muƙaman waɗanda aka roƙa su ka janye da lalama.
6. A bai wa Arewa Ta Tsakiya ko Arewa maso Yamma muƙamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
7. A bai wa Kudu maso Gabas ko Kudu maso Kudu muƙamin Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Wasiƙar Gwamnonin APC Ga Tinubu: Abubuwan La’akari Wajen Zaɓen Shugabannin Majalisar Dattawa Da Ta Wakilan Tarayya:
8. Kafin a bai wa wata shiyya muƙami, a yi la’akari da irin gudummawar da ta bayar wajen samun ƙuri’u a zaɓen shugaban ƙasa.
9. Amma kuma za a iya yin la’akari da neman janyo wani yanki a jika, duk da bai bayar da wata gudunmawar a zo a gani ba, sai a rataya masa wani muƙami, don ya ji a jikin sa cewa ba a maida shi saniyar-ware ba.
10. Matsayar mu a kan Shiyyar Kudu maso Gabas ita ce, yankin bai taɓuka abin ƙwarai a zaɓen shugaban ƙasa ba. Shi ne ma yankin da APC ta fi samun mafi ƙarancin ƙuri’u.
11. Jihohi biyu kaɗai APC ke da Gwamna a Kudu maso Gabas, wato Ebonyi da Imo. To su ɗin ma babu tabbacin ɗorewar su a ƙarƙashin APC. Saboda cikin Nuwamba za a yi zaɓen gwamna a Imo. Kuma zaɓen mace ce da ciki, babu tabbacin ɗan da za ta haifa zai fito da rai ko babu.
12. Wajen rabon muƙamai kamar Shugaban Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai ta Tarayya, a yi la’akari da muƙamin ɗan takara a majalisa. Saboda haka banda sabbin-shigar majalisa a wannan takarar, wato kamar irin su Gwamna Dave Umahi na Ebonyi da Adams Oshiomhole zaɓaɓɓen sanata.
13. Yankin Arewa maso Yamma ya cancanci a ba shi babban muƙami a Majalisa, saboda ya fi kowane yanki bayar da gagarimar gudummawar ƙuri’u. Sannan kuma idan bai samu ba, to yankin zai ce daga saukar Shugaba Muhammadu Buhari ɗan yankin, har APC ta maida shi saniyar-ware kenan.
14. Ya kamata a fahimci cewa APC na da Sanatoci 57 daga cikin 109. Amma akwai zaɓukan sanatoci 5 da ba su kammalu ba.
15. APC na da Wakilan Majalisar Tarayya 162, sauran jam’iyyun hamayya su 7 na da jimlar Wakilai 163. Amma akwai sauran wakilai 31 da za a yi zaɓukan da ba su kammalu ba a kan gurabun su.
16. Masu takarar shugabancin Majalisar Dattawa sun haɗa da: Barau Jibrin (Kano), Abdul’aziz Yari (Zamfara), Dave Umahi (Ebonyi), Orji Uzor Kalu (Abiya), Godswill Akpabio (Akwa Ibom) da Sani Musa (Neja).
17. Masu takarar Kakakin Majalisar Tarayya akwai: Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya na yanzu, Idris Wase (Filato), Yusuf Gagdi (Filato), Muktar Betara (Barno), Sada Soli (Katsina), Tunji Awoniyi (Kwara), Abubakar M. (Jigawa), Ben Kalu (Abiya), Miriam Onucha (Imo), Tajuddeen Abbas (Kaduna) da Aminu Jaji (Zamfara).
18. Mu na kira ga Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa ya yi ganawar gaggawa tare da Mataimakin Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Sanatoci da Mambobin da ke kan kujera, Zaɓaɓɓun Sanatoci da Zaɓaɓɓun Mambobi, Gwamnonin APC da Zaɓaɓɓun Gwamnonin APC da kuma Shugabanin Zartaswar APC domin a shata layin da a za a bi a fitar da shugabannin majalisun biyu cikin ruwan sanyi.
Sai dai kuma ba a sani ba ko tun daga 8 Ga Afrilu da Gwamnonin APC su ka rubuta wa Tinubu wasiƙar, shin ta je wurin sa ko a’a. Tinubu dai ya na ƙasashen Turai ya na hutu.