Zaɓaɓɓun-sanatoci daga Yankin Arewa ta Tsakiya, da su ka ƙunshi jihohin Nasarawa, Kogi, Filato, Kwara, Benuwai da Neja, sun bayyana cewa ba za su amince a ba su duk wani muƙamin da ba Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ba.
Zaɓaɓɓen Sanata Ahmed Wadada ne ya bayyana haka a madadin sauran Zaɓaɓɓun sanatoci na jihohin da aka bayyana a sama, yayin da ya kira taron manema labarai, ranar Juma’a a Abuja.
Wadada wanda aka zaɓa a ƙarƙashin SDP daga Jihar Nassarawa, ya ce matsayar su kenan, kuma babu gudu babu ja da baya.
“Mun haɗu mun yi wa Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa barka da dawowa daga tafiyar da ya yi. Sannan mun ce masa mu na so a yi adalci yayin fitar da shugabannin majalisa ga kowane yanki ko shiyyoyin ƙasar nan.
“Saboda mu na sane da cewa akwai hoɓɓasa da kowace shiyya ke yi, domin ganin ta an fitar da Shugaban, Majalisar Dattawa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisa da Mataimakin Kakakin Majalisa daga yankunan su.
“Don haka mu dai mun san Kudu maso Yamma da Arewa maso Gabas sun fito da Shugaban Ƙasa da Mataimakin Shugaban Ƙasa.
“Saboda haka Arewa ta Tsakiya na kan matsayin cewa muƙamin da kaɗai za ta amince a ba ta, shi ne na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
“Mun jima a kan haka, kuma har yau, har gobe matsayar mu kenan.
“Kuma wanda mu ke so a bai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, shi ne Sanata Sani Musa, ɗan APC daga Jihar Neja.”
Discussion about this post