Shugaban Turkiyya Tayyip Erdoğan, ya shiga jerin shugabannin kasashen duniya wajen mika sakon taya murna ga zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu.
Shugabannin kasashen China Xi Jinping, Firaye Ministan Birtaniya Rishi Sunak, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, Firaye ministan Israila Benjamin Netanyahu, na daga cikin shugabannin da tuni sun aika sakon taya murnanr su ga zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu.
A cikin wasikar taya murna, shugaba Erdoğan wanda ya bayyana Asiwaju Tinubu a matsayin dan uwa, ya bukaci hadin kai da hadin gwiwa da zai kara dankon zumunci tsakanin Turkiyya da Najeriya.
A cikin wasikar Erdoğan ya kuma jaddada muhimmancin Najeriya a matsayinta na kasa mafi karfi a nahiyar Afirka tare da yi wa Asiwaju Tinubu fatan samun nasarar gudanar da mulki wanda zai kawo ci gaba ga al’ummar Najeriya.
“A madadin al’ummar kasar Turkiyya da ni kaina, ina mika sakon taya murna ga mai girma zababben shugaban Najeriya b a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
“Ba ni da tantama cewa, da kokarinmu na hadin gwiwa, za mu bunkasa dangantakar abokantaka, da kara samun hadin kai a tsakanin kasashenmu, domin samun moriyar juna.
” Ina yi maka fatan alkhairi da lafiya tabbatacciya sannan kuma da yi wa illahirin ‘yan Najeriya addu’ar Allah ya kara dankon zumunci da soyayya a tsakanin mu baki daya.
Discussion about this post