Yayin da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), Okey Wali ya cika kwanaki bakwai a hannun masu garkuwa, su kuma shugabannin NBA da ke kan muƙami, sun ziyarci iyalan Okey Wali wanda masu garkuwa ke tsare da shi, bayan kama shi a Jihar Ribas.
Shugaban NBA na Ƙasa, Yakubu Maikyau ne ya jagoranci tawagar har gidan Wali wurin iyalin sa a Fatakwal.
Maikyau ya roƙi waɗanda su ka yi garkuwa da shi cewa su tausaya su sake shi, domin ya kai shekaru 64 a duniya.
Kingsley Wali ƙani ga Okey da kuma matar Wali ɗin ce su ka tarbe su.
Ba a dai san abin da su ka tattauna ba. Amma daga can sun ziyarci matar Peter Odili, wadda ita ce Shugabar Shugaban Kwamitin Dattawan Ƙungiyar Lauyoyi.
Tsohuwar Mai Shari’a ce a Kotun Ƙoli, wadda ta yi ritaya ba da daɗewa ba.
Makonni biyu da su ka wuce ne mu ka kawo rahoton cewa mahara sun arce da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, Okey Wali.
Masu garkuwa sun gudu da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, Okey Wali daga gidan sa.
An arce da shi da ƙarfin tsiya daga gidan sa, a safiyar Litinin.
Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa ce ta bayar da sanarwar tabbacin kama yin garkuwar da shi a ranar Talata.
Okey dai babban lauya ne, wato SAN, kuma an kama shi kan hanyar Obio/Akpor cikin Jihar Ribas.
Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa na yanzu, Yakubu Maikyau ya roƙi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Alƙali Usman da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ribas su yi iyakar ƙoƙarin tabbatar da ceto tsohon shugaban lauyoyin na Najeriya.
Wali Okey ya yi shugabancin NBA tsakanin 2012 zuwa 2014.
Sanarwar ta ce Wali Okey ya Yi wa ƙungiyar lauyoyi aiki tuƙuru a zamanin da ya yi shugabancin NBA.
Discussion about this post