Gwamna Nysome Wike na Jihar Ribas ya bayyana cewa zai kammala mulkin sa a ranar 29 Ga Mayu ya na mai godiya da farin cikin cikar burin sa da alfaharin sauke nauyin gudanar da ayyukan ci gaba a faɗin dukkan ƙananan hukumomin da ke faɗin jihar.
Wike ya yi wannan bayani a wurin taron addu’o’in fatan alheri da PDP reshen Jihar Ribas ta shirya wa Wike, kuma aka gudanar da babban cocin Saints Anglican Cathedral.
“Daga makaho sai maƙiyi na kaɗai za su ce ban samar da gagarumin ci gaba a faɗin jihar nan ba.
“Idan siyasar ka ba ta neman kawo ci gaban jama’a ba ce, to kai babbar matsala ce ga jama’ar ka. Yanzu kan masu zaɓe ya waye. Tilas nan da shekara huɗu cikin 2027 ku bayyana wa jama’a rahoton ayyukan ci gaba da ku ka yi masu, idan dai har ku na so su sake zaɓen ku.”
Wike ya danganta nasarar da PDP ta samu a jihar da irin ayyukan rasa ƙasa, gwamnati mai tsari da kuma daidaiton da maza da mata su ka samu bakin gwargwado a gwamnatin sa.
Ya ce kowace ƙaramar hukuma mace ce Mataimakiyar Shugabar Ƙaramar Hukuma, sannan kuma akwai kansila mata biyar a kowace ƙaramar hukuma. Kuma akwai sanata mace da ‘yan majalisar tarayya mata da aka zaɓa kwanan nan.
Daga nan ya yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan Ribas, Siminialayi Fubara da gwamnatin da zai kafa kada su riƙa tsayawa ɓata lokaci su na kula ‘yan adawa.