A ranar 14 Ga Afrilu, 2014 ne, shekaru 9 kenan bayan da Boko Haram su ka kutsa Makarantar Sakandare ta Mata da ke Chibok, inda su ka kwashi ɗalibai mata 276, har yau 14 ga Afrilu, 2023, akwai sauran ɗalibai mata har 98 a hannun ‘yan ta’addar Boko Haram.
Bayan garkuwa da ɗaliban, an ci gaba da yin garkuwa da ɗaliban sakandare maza da mata a Arewacin Najeriya, a garuruwa ko jihohi daban-daban, saboda kasa magance darasin da hukumomin Najeriya su ka ɗauka, tun bayan harin Chibok ɗin da aka kai, wanda ya girgiza ba Najeriya kaɗai ba, har ma duniya baki ɗaya.
Kungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Amnesty International ce ta tabbatar da haka a yau.
Tun bayan garkuwa da ɗaliban Chibok, ƙananan yara da mata na ci gaba da fuskantar uƙuba a hannun ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga masu yin garkuwa da mata, su na yi masu fyaɗe, su kashe su ko kuma su tilasta masu yi masu auren dole a tsakanin su a cikin daji.
Sai dai kuma har yau mahukuntan Najeriya ba su yi wani ƙwaƙƙwaran bincike ko da sau ɗaya ba, domin gano matsalar tsaron da ke sa ƙananan yara ke faɗawa ƙangin azabtarwa a hannun Boko Haram da ‘yan bindiga.
“Iyayen ɗaliban Chibok 98 da ake tsare da su hannun Boko Haram tsawon shekaru 9, su na da yaran da ‘yan bindiga su ka riƙa garkuwa da su, har da su ma yaran da aka yi garkuwar da su, duk su na cikin halin matsanancin jimami, damuwa, tararrabi, ƙuncin rayuwa, saboda sanin da su ka yi cewa yaran su na hannun wasu matsiyatan marasa imani masu gallaza masu tare da azabtar da su, cewar Isa Sanusi, Mataimakin Darakta na Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam a Najeriya.
“Tuni an yi latti, kuma lokaci ya ƙure da mahukuntan Najeriya ya kamata a ce sun ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ko matakan daƙile Boko Haram da ‘yan bindiga.
Akwai haƙƙi kan Najeriya na tabbatar da ta kare rayukan ƙananan yara. Sannan kuma rashin hukunta masu aikata wannan ta’addanci ya na matuƙar ƙara ruruta wutar ta’addancin. Ba za a iya tabbatar da adalci ba, har sai an maido dukkan ɗaliban da ke hannun ‘yan Boko Haram da ‘yan bindiga, sannan kuma an hukunta dukkan masu hannu a cikin wannan ta’addanci.”
Tsakanin Disamba 2020 da Maris 2021, aƙalla an samu rahotanni kwasar ɗalibai sau biyar a makarantu daban-daban a Arewacin Najeriya. Kama daga Ƙanƙara, Kagara, Tegina da Yawuri, Jangebe, Damishi Kaduna. Sannan kuma barazanar kai irin waɗannan hare-haren kwasar ɗalibai mata da maza ya haifar da kulle makarantu sama da 600 a Arewacin Najeriya.
Iyayen ɗaliban Chibok 98 da ke hannun Boko Haram har yau ɗin nan, sun bayyana cewa a yanzu sun ma haƙura da tunanin za a iya ceto masu yaran su.
Ɗaya daga cikin waɗanda su ka kuɓuta, ta shaida wa Amnesty International cewa, “kada Gwamnatin Najeriya ta manta da sauran ɗalibai 98 da ke hannun Boko Haram. Ya kamata a hanzarta ceto su.”
Su kuma iyayen yaran abin da ya fi damun su shi ne yadda Boko Haram su ka tilasta wa yaran auren su ba don su na so ba. Ga shi kuma rayuwa su ke yi a cikin daji. Sannan kuma ga azabtawa da wulaƙantarwa.
Ɗaya daga cikin iyayen ya shaida wa Amnesty International cewa takaicin mu fa ba zai gushe ba har abada. Saboda yanzu haka ‘yan mata 14 da su ka dawo, sun dawo mata da yara 24. Mun zama jikokin yaran da ba mu san iyayen su ba. Kun ga takaicin mu na ma ruɓanya kenan. Ga wahalar ciyar da su, tufatarwa da kuma gaganiyar ilmin su da kula da lafiyar su. Baya kuma ga ƙududun baƙin cikin da ke tattare da mu, haɗi da yadda al’umma ke ƙaurace wa iyayen yaran.”
Iyayen ɗaliban Chibok da har yanzu ke hannun Boko Haram, sun shaida wa Amnesty International cewa tuni gwamnatin Najeriya ta daina sauraren su. Kuma ta yi watsi da su.
Discussion about this post