Jam’iyyar APC a ranar Litinin ta nemi Kotun Shari’ar Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPC) a Abuja cewa ta kori ƙarar da jam’iyyar LP tare da ɗan takarar ta, Peter Obi su ka shigar kan nasarar Bola Tinubu a zaɓen 2023.
A takarar jayayyar da APC ke yi kan rashin cancantar Obi ya shigar da ƙara, ɗaya daga cikin lauyoyin mai suna Thomas Ojo, ya ce babu wani dalilin da zai sa Peter Obi ya kai ƙara kan rashin cancantar Tinubu tsayawa takara, domin shi Peter Obi ɗin ne ma bai cancanta ba.
Daga sauran dalilan shigar da ƙarar da Obi ya yi baya ga ƙorafin rashin cancantar Tinubu da Kashin Shettima, akwai zargin an yi maguɗi a jihohi 11, sai kuma azarɓaɓin da ya ce INEC ta yi ta bayyana sakamakon zaɓe, ba tare da ta tattara kuma ta tura sakamakon daga na’urar tantance masu rajistar zaɓe ta BVAS zuwa Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta iReV ba.
Yadda APC Ta Yi Wa Peter Obi Zabari Da Ƙungiya A Kotu:
1. ” Shirme Peter Obi ya ke yi da ya garzaya kotu jayayyar rashin cancantar takarar Tinubu da Shettima, domin ai shi ma bai shiga jam’iyyar LP an yi takarar fidda gwani da shi ba kwanaki 30 kafin zaɓen fidda gwani, kamar yadda Dokar INEC ta gindaya.”
2. ” Har ranar 24 Ga Mayu, 2022 Peter Obi na cikin PDP, bai koma LP ba.”
3. ” A cikin watan Afrilu an tantance Peter Obi cikin ‘yan takarar fidda-gwanin PDP.”
4. ” An wanke Peter Obi a PDP, aka ba shi damar fitowa takarar zaɓen shugaban ƙasa a lokacin ya na cikin PDP.”
5. ” Peter Obi ya fita daga PDP ranar 24 Ga Mayu, 2022 ya shiga LP ranar 27 Ga Mayu, 2022.”
6. ” LP ta yi zaɓen fidda gwani ranar 30 Ga Mayu, aka zaɓi Peter Obi ɗan takarar ta, kwanaki uku kacal bayan shigar sa jam’iyyar. Hakan kuwa ya karya Dokar Zaɓe Sashe na 77(3).”
7. ” Zaɓen Peter Obi ɗan takarar LP cikin kwanaki uku da shigar sa LP, hakan ya tabbatar da babu sunan sa a jerin ‘yan takarar da LP ta miƙa wa INEC kwanaki 30 kafin zaɓen fidda gwani kamar yadda Dokar INEC ta gindaya.”
8. ” Sunan Peter Obi na cikin ‘yan takarar da PDP ta tantance a ranar 29 Ga Afrilu, ta miƙa wa INEC. Don haka sunan Obi na can cikin ‘yan takarar PDP da aka aika wa INEC kwanaki 30 kafin zaɓen fidda gwani.”
9. ” Babu dalilin da Peter Obi zai kai ƙara, domin lokacin da ya shiga LP, babu sunan sa a cikin rajistar ‘yan takarar LP da ke hannun INEC kwanaki 30 kafin zaɓen fidda gwani.”
10. ” Masu ƙara da kan su, wato LP da Peter Obi, sun rattaba a kwafen ƙarar da su ka shigar cewa Atiku Abubakar na PDP ne ya zo na biyu da ƙuri’u 6,984,520, shi kuma Obi ya zo na uku da ƙuri’u 6,101,533.”
11. ” Tunda Obi ya yarda Atiku ya fi shi yawan ƙuri’u, tilas ya haɗa da Atiku da PDP cikin waɗanda shi Obi ɗin ya ke ƙara. Domin ba shi Obi ɗin ne ya zo na biyu ba.”
12. ” Babu yadda za a yi kotu ta saurari ƙarar da Peter Obi ya shigar, sai fa idan ta soke sakamakon Atiku Abubakar da ya zo na biyu a zaɓen, domin wanda ya zo na uku ba zai taɓa zuwa ya yi rinton nasara ba, alhali ga wanda ya zo na biyu a gaban sa.”