Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta yanke shawarar yin bincike domin su gano yadda aka karkatar da naira biliyan 20 ta hanyar biyan kuɗaɗen ga ‘yan kwangilar da babu su, sunayen bogi ne.
Amincewa a yi binciken ya biyo bayan wani ɗan majalisa na APC daga Kano, Ibrahim Kawu, a ranar Alhamis.
Kawu ya miƙe tsaye ya nemi a gaggauta yin bincike domin a gano yadda NNPCL ya biya Naira biliyan 20 ga kamfanin da babu shi, babu alamar sa.
“Rahotanni sun nuna wasu ma’aikatan NNPC sun biya Naira biliyan 20 ga kamfanin da babu shi babu dalilin sa. Sunan kamfanin da aka danƙara wa kuɗaɗen wai Messrs Safaya.” Inji shi.
Kawu ya ce ya zama tilas su yi bincike domin a gano wannan ɓarusa, ta yadda Majalisar Tarayya za ta taya Gwamnatin Tarayya yaƙi da cin hanci da kuma rashawa.
NNPCL dai ta ƙaryata zargin ta biya kuɗin ga kamfani bogi. Wato a ce Sahara Reporters da ta buga labarin ƙarya ta ke yi.
Amma dai NNPCL ya ce akwai wasu kuɗaɗe Naira biliyan 18 da ake rigima da Gwamnatin Jihar Ogun kan kuɗaɗen. Kuma maganar yanzu haka ta na kotu.
An dai bai wa kwamitin da zai binciko kuɗaɗen makonni huɗu domin ya kammala bincike kuma ya miƙa rahoto.