Mazauna garin Ikare a Jihar Ondo sun wayi gari safiyar Litinin ana harbe-harben bindigogi ko ta ina a cikin garin, yayin da aka tabbatar da bindige mutum ɗaya.
Baya ga harbe-harben bindigogi, an yi ƙone-ƙone a garin mai daɗaɗɗen tarihi wato Ikare Akoko.
An tabbatar da rahoton ji wa mutane da dama raunuka tare da ƙone dukiyoyi masu tarin yawa.
Duk da ana tabbatar da cewa an kashe mutum biyu a hargitsin, su kuma ‘yan sanda sun ce mutumin da aka harba ɗin ma ya na nan da ran sa, ana yi masa magani a asibiti.
Yayin hargitsin dai harkoki sun tsaya cak, yayin da mutane da dama su ka yi ta tserewa su na ficewa daga garin.
Matasan da ke yawo kwararo-kwararo su na harbi, sun kuma banka wa gidaje wuta.
Mazauna garin waɗanda suka yi hira da wakilin mu, sun ce babu jami’an tsaron da su ka kai ɗauki a lokacin da ake tarzomar.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami ta ce yanzu garin ya lafa, zaman lafiya ya dawo.
Ta ce jami’an ‘yan sanda na ci gaba da binciken musabbabin tarzomar.
Idan na a manta ba, gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin binciken rikicin mazauna garin da kuma rikicin addini, wanda har ta kai ga an rufe babban masallacin garin. Amma dai har yanzu kwamitin bai damƙa wa gwamnatin Ondo rahoton sa ba.
Kafin nan dama an rufe makarantun garin kuma an sa tsaro.
Garin Ikare Akoko ya faɗa cikin rikicin limancin babban masallacin garin.
A ƙarshen watan Maris ne Gwamnatin Jihar Ondo ta faɗi dalilin da ya sa ba za ta buɗe masallacin Ikare a cikin watan Ramadan ba.
Gwamnatin Jihar Ondo ta bayyana dalilin da ya sa ba za ta bada umarnin buɗe Babban Masallacin Ikere ba domin a yi sallolin tarawy da sauran ibadu a cikin watan Ramadan.
Gwamnatin Jihar Ondo dai ta kulle babban masallacin tun a cikin watan Oktoba, 2022, biyo bayan wani mummunan hargitsi da ya afku sanadiyyar tsige babban limamin masallacin na Ikare Akoko da aka yi.
Gwamnatin ta ce ba za ta buɗe masallacin ba har sai ɓangarorin da ke rikici da juna sanadiyyar cire babban limamin sun sasanta kan su tukunna.
“Gwamnati ta amince ta janye dokar hana fita,sanadiyyar mummunan tashin hankalin da ya afku. Amma ba za ta buɗe masallacin a cikin watan Ramadan kamar yadda ake ta roƙo a yi ba, har sai ɓangarorin biyu masu rikici sun sasanta kan su tukunna.” Haka Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Ondo ya sanar.
Asalin rikicin dai ya faro ne lokacin da Majalisar Malaman Ikere tare da goyon bayan Sarkin Ikere, wato Olukare na Ikare, Saliu Momoh IV, su ka tsige Babban Limamin Ikare mai Sallah a masallacin, Abubakar Muhammad.
Bayan cire shi, sai Babban Kwamitin Kula da Harkokin Musulunci na Jihar Ondo ya ƙi amincewa da cire Liman Abubakar da aka yi. Hakan kuwa ya haifar da tsaikon komai a tsakanin ɓangarorin biyu.
Duk wani roƙon a maida limamin da aka yi wa malaman Ikare dai bai shiga kunnen su ba.
To lamarin ya haifar da ruɗani da hargitsi har sai da gwamnatin Ondo ta ƙaƙaba dokar hana fita a garin.
Shi dai Kwamishinan Yaɗa Labaran Ondo, Bamidele Ademola-Olateju ya ce gwamnati ba za ta buɗe masallacin ba, sai an samu sasanci tsakanin bangarorin biyu da ke husuma da jayayya.