Wasu mahara ɗauke da zabga-zabgan bindigogi sun arce da Kwamishinar Ƙidayar Jama’a ta Tarayya, Gloria Izonfuo.
Gloria ita ce Kwamishinar Kidaya ta Jihar Bayelsa.
‘Yan Sanda a Jihar Ribas ta bakin kakakin su, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da garkuwar da aka yi da Kwamishinar ta NPC a ranar Litinin.
Ta ce an yi garkuwa da Izonfuo tare da direban ta da wata ‘yar aikin ta a daidai mahaɗar Ogbakiri.
Su ukun su na kan hanyar komawa Fatakwal bayan sun je garin Brass cikin jihar Bayelsa.
Grace Iringe-Koko ta ƙara da cewa an baza ƙwararrun ‘yan sanda su tabbatar sun ceto su daga hannun masu garkuwa.
Wadda aka sace ɗin tsohuwar shugabar ma’aikatan jihar Bayelsa ce da ta yi ritaya.
Masu garkuwar 7dai sun buƙaci a biya su Naira miliyan 500 kafin su sake ta.
A jihar Ribas inda aka yi garkuwa da Kwamishinar Ƙidaya, a can ne dai kuma cikin makon jiya wasu mahara su ka arce da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, Okey Wali.
Masu garkuwa sun gudu da tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, Okey Wali daga gidan sa.
An arce da shi da ƙarfin tsiya daga gidan sa, a safiyar Litinin.
Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa ce ta bayar da sanarwar tabbacin kama yin garkuwar da shi a ranar Talata.
Okey dai babban lauya ne, wato SAN, kuma an kama shi kan hanyar Obio/Akpor cikin Jihar Ribas.
Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa na yanzu, Yakubu Maikyau ya roƙi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Alƙali Usman da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ribas su yi iyakar ƙoƙarin tabbatar da ceto tsohon shugaban lauyoyin na Najeriya.
Wali Okey ya yi shugabancin NBA tsakanin 2012 zuwa 2014.
Discussion about this post