Masu garkuwa da mutane sun saki tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nassarawa, Onje Gye-Wado.
An yi garkuwa da Gye-Wado tun a ranar 7 Ga Afrilu, bayan an arce da shi daga cikin gidan sa da ke garin Wamba, Jihar Nasarawa.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da sakin tsohon Mataimakin Gwamnan a ranar Litinin, a Lafiya.
Gye-Wado ya yi mataimakin gwamna ga Abdullahi Adamu, daga 1999 zuwa 2003.
An sake shi ranar Lahadi wajen ƙarfe 9 na dare, ya koma cikin iyalin sa.
Nansel ya ce har zuwa yanzu dai ba a kama ko mutum ɗaya da ake zargi ba tukunna, kuma ‘yan sanda ba su da masaniyar shin sai da aka biya kuɗin fansa sannan aka sake shi, ko kuwa haka siddan su ka ce ya tafi gida.
Sai dai Kakakin Yaɗa Labaran na ‘Yan Sandan, ya ce masu garkuwa sun saki dattijon ne saboda matsin-lambar da hadakar jami’an tsaro ke yi masu.
Discussion about this post