Hukumar hana sha da safarar muggan kwayoyi na kasa NDLEA ta kama wata mata mai ciki Rabetu Abdulrasak mai shekara 24 tare da wani gurgu Shehu Adams dauke da tulin muggan kwayoyi a jihar Edo.
Kakakin hukumar Femi Babafemi ya ce an kama wadannan mutane ranar Asabar a Agbede dake karamar hukumar Etsako ta Yamma da kilo giram sama da 14 tare da su.
Da yake sanar wa manema labarai ranar Lahadi a Abuja Babafemi ya ce an kama mutanen da ganyen wiwi, methamphetamine, kwayoyin tramadol da swinol.
Bayan haka kakakin hukumar NDLEA ya ce dakarun hukumar sun kama wata dalibar kwalejin kimiya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya dake Ilaro a jihar Ogun Isoyo Iveren-Susan mai shekara 22.
Ya ce an kama Susan yayin da take siyar da haramtattun kwayoyin a kofar shiga kwalejin ranar Asabar.
Babafemi ya ce an kama dalibar da ruwan magani tari na codine mai nauyin milligram 1,100 da giram 283 na ganyen wiwi.
Daga nan Kuma ya ce a jihar Legas hukumar ta kama wasu mutane biyu Nonso Peter dan shekara 21 da Bright Chibike dan shekara 23 da kilo giram 43.4 na ganyen wiwi a Ile-Epo dake Abule Egba ranar Juma’a.
A jihar Katsina ranar Lahadin da ta gabata hukumar ta kama kwalabe 1,730 na maganin codine daga wurin wani Bishir Sa’adu a cikin garin Katsina.
Sannan a wannan rana Kuma hukumar ta kama Muhamadu Yusuf a cikin motar hayar Kano zuwa Katsina dauke da kwayoyi 8,000 na Tramadol.
Daga nan Babafemi ya ce NDLEA a jihar Kaduna ranar Alhamis din da ta gabata ta kama wani gida a Sabon Garin Zaria da ake hada kwayar ‘Mist Potassium Citrate’.
Ya ce hukumar ta kama mutumin dake da wurin Christopher Agodi tare da katan 102 na kwayoyin dake dauke da kwalabai 2,448.
Babafemi ya ce hukumar ta kama wani Salisu Abdullahi mai shekara 25 a hanyar Kaduna zuwa Abuja dauke da ganyen wiwi mai nauyin kilo gram 11.7 da aka boye a cikin jarka daga Fatakwal za a kaisu Kano.
Hukumar a ranar Asabar ta kama Atiku Abubakar mai shekaru 22 dauke da kg 28 na ganyen wiwi a cikin motar haya daga Legas zai kansu garin Shinkafi jihar Zamfara.