Hukumar yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi NDLEA ta bankaɗo kamfani da ake hada A-kuskura a garin Mubi na Jihar Adamawa.
Kakakin hukumar Femi Babafemi ne ya sanar da haka a sanarwa da ya saka wa hannu aka buga a shafin hukumar a yanar gizo.
Babafemi ya bayyana cewa a diran wa ma’aikatan kamfanin ne a harabar kamfanin a daidai suna aikin haɗa wannan magani.
Bayan haka NDLEA ta ce ta kai samame a wani gini da ke cikin wani daji a garin Ala kusa da Akure a babban birnin jihar Ondo inda ta gano buhunan ganyen tabar Wiwi masu yawa, sannan kuma hukumar ta kama dauri 126 na tabar wiwi nau’in ‘Canadian Laud’ cikin wata mota kirar Corolla da aka yi safararta daga kasar Kanada wanda aka kama a tashar ruwa ta Tincan da ke Legas.
Benuwai
Hukumar NDLEA ta kama kwalaben maganin tari na Kodin wadanda nauyinsu ya kai kilogiram 117.3 da ake zargin wani dillalin muggan kwayoyi ne ya jefar da su a lokacin da ya doso wani shingen binciken NDLEA da ke hanyar Enugu zuwa Otukpo.