Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya bayyana cewa Najeriya ta na buƙatar mai kishin da ya iya tafiyar da mulki, kuma zai yi aiki tuƙuru a kai ga ci, ba wai sai mai tsoron Allah da taƙawar-zuci ba.
Fashola ya yi wannan kakkausan furuci ne a matsayin kariya ga Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ganin yadda a kullum ake ta fitowa da zarge-zargen rashin cancantar sa tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Ya yi wannan bayanin ne ganin yadda kwanan nan kuma aka fito da wani sabon tone-tone a kan Tinubu, wanda aka yi zargin cewa ya na da katin shaidar zama ɗan ƙasar Guenea, baya ga kasancewar sa ɗan Najeriya.
Fashola ya ce shi dai a iyar sanin sa Tinubu ɗan Najeriya ne, bai san ya na da fasfo na shaidar kasancewar sa ɗan Amurka ko wata ƙasa ba.
“Sannan kuma a iyakar sani na, ai dokar Najeriya ta bai wa kowane ɗan Najeriya damar mallakar shaidar zama ɗan wata ƙasa, baya ga ƙasar sa ta haihuwa, wato ‘dual citizen’.
“Na san dai Tinubu ya na da fasfo ɗaya na kasancewar sa ɗan Najeriya. Amma ban san ko ya na da na wata ƙasa ko ba shi da shi ba. Na san dai ya yi zama a ƙasashen waje a lokacin da ya yi gudun hijira.”
“Ban sani ba ko ya na da fasfo ɗin shaidar zama ɗan ƙasar Amurka. To shin ma mene ne alaƙar wannan da sakamakon zaɓe? Ni dai a iyakar sani na, Dokar Najeriya ta ba kowa damar zama ɗan wata ƙasa, baya ga kasancewar sa haifaffen ɗan Najeriya. Ko ba haka ba ne?”
Masu tone-tonen cewa Tinubu na da fasfo ɗin zama ɗan wata ƙasa, baya ga Najeriya, sun buga hujja da Sashe na 137 na Kundin Dokokin Najeriya, wanda su ka ce ya haramta cewa:
“Sashe na 137 (1): Wanda ya mallaki fasfo ɗin zama ɗan wata ƙasa, baya ga na sa na shaidar haifaffen Najeriya ne, to ba zai cancanci a zaɓe shi shugaban ƙasa ba.
“Idan zai tsaya takarar shugaban ƙasa, to ya sanar da hukuma a rubuce cewa ya yi watsi da wancan fasfo na wata ƙasa da ya ke da shi, ya riƙe na Najeriya, ƙasar sa ta haihuwa.”
Har yanzu dai Tinubu bai yi magana a kan lamarin ba. Dama kuma rahotanni sun tabbatar da cewa Tinubu aminin tsohon Shugaban Ƙasar Guinea ne, Apha Conde.
Cikin 2015, Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar zaɓen Conde, wanda sojoji su ka yi wa juyin mulki cikin 2021.
‘Mulki Ba Sai Tsoron Allah Da Taƙawa Ba’ – Fashola:
Fashola ya ce Najeriya ba ta buƙatar sai mai tsoron Allah ko wanda ba ya saɓo. Ya ce wanda Najeriya ke buƙata shi ne mai kishin ƙasa, wanda zai yi aiki tuƙuru ya kai ƙasar gaci.
Sannan ya ce kuma dukkan zarge-zargen da ake yi wa Tinubu sun zama tatsuniya, domin har yau masu ƙorafe-ƙorafen sun kasa gabatar da gamsasshiyar hujjar da za ta gamsar da zarge-zargen su ko yarfen da su ke yi masa.
“Ni dai a tunani na, ina ganin duk an wuce wannan wurin. Mai yiwuwa wata karama ce Allah zai saukar mana ta dalilin shugabacin Tinubu. Mai yiwuwa daga mulkin sa ne Najeriya za ta kama nagartacciya kuma miƙaƙƙar hanyar kaiwa gaci na har abada.” Cewar Fashola.