‘Yan ta’addar ISWAP na kusa ga fara yin amfani da na’urar ‘drones’ domin kai hare-hare a Yankin Tafkin Chadi. Irin wannan salon maƙala wa na’urar jirgin da ke tuƙa kan sa da kan sa, zai iya ƙara munin yaƙin Boko Haram a yankin.
Cibiyar Nazarin Matsalar Tsaro ta ISS ce ta nuna cewa sarrafa na’urorin kyamarar ‘drones’ domin su riƙa maƙala mata muggan makamai da bama-bamai su na kai hare-hare.
ISS ta ce ISWAP na nazarin da binciken iyar nauyin makami ko ban ɗin da kowane ‘drone’ ɗaya zai iya ɗauka.
Sannan kuma ISWAP su na nazarin iyar nisan zangon da drone zai iya yi idan da kuma iyar tsawon lokacin da zai iya yi ya na shawagi a ƙasa ba tare da ya faɗo ƙasa ba.
ISS ta ce hare-haren da ISWAP ke shirin kaiwa ba a kan sojoji kaɗai zai tsaya ba, har ma a cikin fararen hula.
Zuwa yanzu dai iyar amfani da ‘drones’ ɗin da ISWAP ke yi, bai wuce farfaganda ba, sai sintirin leƙen asiri da kuma aika aika saƙonnin sadarwa da sauran irin su
ISS ta yi bincike ne ta hanyoyi daban-daban, ciki har da hira da tsoffi ko tubabbun su da makusantan su, ta hanyar wayoyin zamani na Android da soshiyal midiya, irin su shafin zumunta na Telegram, WhatsApp da sauran su.
ISS ta ce ta yi binciken cewa dukkan kayayyakin da ta lissafa a sama, wani gungun ‘yan ta’adda a ƙarƙashin Abba Yusuf (Abu Rumaisa) ke nazarin su. Abu Rumaisa da ke kula da ɓangaren.
Haka kuma su na wani tubabben ɗan ta’adda ya shaida wa ISS cewa ISWAP na amfani da Wi-Fi na Thuraya, kuma su na kashe dala 6,000 duk wata wajen sayen data.