Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce kimanin mutane 1,052 aka kashe, an sace mutum 4,227, yayin da 648 suka jikkata a hare-haren ta’addanci a shekarar 2022.
Aruwan ya bayyana haka ne a ranar Laraba a yayin gabatar da rahoto kan halin tsaro a jihar a shekarar 2022.
Rahoton mai taken “Halin Tsaro a Jihar Kaduna daga ranar 1 ga Janairu zuwa 31 ga Disamba, 2022,” ya kunshi batutuwan tsaro da suka hada da Fashi da makami, ta’addanci, garkuwa da mutane, fyade da ɓarayin shanu, rikicin kabilanci da hare-haren wuce gona da iri. , da kuma harin ramuwar gayya.
Alkaluman da aka gabatar sun samo asali ne daga rahotannin yau da kullun na hukumomin tsaro da suka haɗa da Sojoji na Ruwa da na Sama ‘Yan Sanda, Jami’an Tsaron na (DSS), Sibul Difens (NSCDC), Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA) da Hukumar Bijilante na Jihar Kaduna (KADVS) – shugabannin al’umma (shugabannin unguwanni, hakiman kauye, hakimai, sarakuna da masarautu) da sahihan hanyoyin sadarwar jama’a.
“ Saboda haka alkaluman da gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar a nan sahihai ne kwarai. Inji Aruwan.
A cikin mutane 1,052 da aka kashe, Aruwan ya ce 947 maza ne, 82 mata ne yayin da 23 kuma yara kanana ne.
Daga cikin wadanda aka kashen, 641 sun fito ne daga tsakiyar jihar yayin da 349 suka fito daga Kudancin jihar. Rahoton ya bayyana cewa an kashe mutane 62 a yankin Arewacin jihar.
Daga cikin jimillar mutane 4,227 da aka yi garkuwa da su, 2,606 maza ne, 1,395 kuma mata ne yayin da sauran 226 yara kanana ne.
Har yanzu dai shiyyar Kaduna ta tsakiya ce ke kan gaba a yawan wadanda aka sace da mutane 3,112 yayin da yankin kudancin Kaduna ke da mutane 925 da aka sace sannan yankin arewacin jihar ke da 190.
Sannan kuma an kashe wasu gaggan ƴan bindiga da dama.