Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da harin da ‘yan bindiga su ka sake kai wa a kauyen Runji dake karamar hukumar Zangon Kataf.
Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan wanda ya tabbatar da haka ya ce mutane da dama sun mutu a harin da ya auku ranar Asabar.
Aruwan ya ce rundunar sojin Najeriya ce ta sanar wa gwamnati sai dai a Lokacin gwamnati bata da tabbacin yawan mutanen da suka mutu a harin.
“Rahoton ya nuna cewa wasu mutane da dama sun ji rauni kuma Kona gidaje da dama a dalilin harin.
“Jami’an tsaron sun yi bata kashi da maharan a lokacin da suke wannan aika-aika kuma ba su ji da daɗi ba.
Ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya Yi tir da abin da ya faru sannan ya tabbatar cewa jami’an tsaro na gudanar da bincike domin kamo maharan.
“Ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalai da ƴan uwan waɗanda suka rasa wani nasu sannan ya yi addu’ar Allah ya kawo sauki ga wadanda suka ji rauni.
“Da zaran jami’an tsaron sun kammala bincike gwamnati za ta sanar da yawan mutanen da suka mutu da kuma waɗanda suka ji rauni a dalilin harin.
Wannan shine karo na biyu da ‘yan bindigan ke kai wa mutane hari a karamar hukumar a cikin mako daya.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan bindiga suka kashe mutum 8 a harin da suka kai karamar hukuma a makon jiya.
Shugaban kungiyar Atiyap Sam Timbuwak ya ce maharan sun afka kauyen su da misalin karfe 9 na safiyar Laraba ne.