Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa masu lambobin waya ko wayoyin hannu a Najeriya daidai ƙarshen 2022, sun kai mutum miliyan 222.5.
Kenan ƙididdigar ta nuna an samu ƙarin mutum miliyan 27.1 daga adadin mutum miliyan 195.5 masu waya ko lambar waya a ƙarshen 2021.
NBS ta yi wannan bayanin a cikin rahoton ƙididdiga da ta fitar na kowace jiha, na watanni huɗun ƙarshen 2022, rahoton da ta fitar ranar Litinin a Abuja.
NBS ta ce ta yi rikodin na masu amfani da intanet har mutum miliyan 154.9 a ƙasar nan a ƙarshen 2022.
Hukumar ta ce an samu ƙarin masu amfani da intanet kenan idan aka kwatanta da ƙarshen 2021 lokacin da masu amfani da intanet ɗin su 142 ne.
Jihohin Da Su Ka Fi Amfani Da Wayoyi:
1. Jihar Legas miliyan 26.5.
2. Jihar Ogun miliyan 13.
3. Jihar Kano miliyan 12.4.
37. Bayelsa miliyan 1.6
Rahoton har ila yau ya nuna Legas ɗin dai ce ta fi yawan masu amfani da intanet a ƙarshen 2022, har mutum miliyan 18.7.
Jihar Ogun ce ta biyu da mutum miliyan 9.2, sai Kano mai miliyan 8.5. Jihar Bayelsa ce ƙarshe mai mutum miliyan 1.1.
NBS ta ce mafi yawan masu amfani da lambobin waya, sun fi amfani da MTN.
Discussion about this post