Gwamnan Jihar Benuwai Samuel Ortom, ya maida wa Fadar Shugaban Ƙasa kakkausan raddi dangane da matsalar tsaro da kashe-kashen da ake fama a Jihar Benuwai. Ortom ya ce Shugaba Buhari ya sane ya kauda kai daga magance matsalolin da kuma kasa gano makasan da ke addabar jihar.
Samuel Ortom ya kuma zargi Buhari da hana Benuwai kuɗaɗen da ke haƙƙin ta, sannan kuma ya ce Buhari ɗin ya damalmala zaɓen 2023 a jihar Benuwai, ta yadda ya taimaka wa jam’iyyar sa APC, ta yi nasara a zaɓen gwamnan jihar.
Ortom ya yi wa Buhari wannan raddin ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna mai suna Nathaniel Ikyur ya fitar a Makurɗi a ranar Alhamis.
A ranar Laraba ce dai Fadar Shugaban Ƙasa ta nesanta Buhari daga masaniya ko rashin maida hankali domin kawo ƙarshen kashe-kashen da ake yi a Benuwai.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu, ya ce Ortom ya tsarma siyasa a lamarin matsalar tsaron Jihar Benuwai.
“Da a ce Ortom, gwamnan da ya kwashi buhun kunya a zaɓen 2023 da maida hankali wajen abin da ya damu Jihar Benuwai, maimakon maida rikicin siyasa, to kuwa da abin bai kai haka ba.”
Garba Shehu ya buga misali da jihohin Taraba da Nasarawa da Babban Birnin Tarayya, waɗanda a yanzu haka su na kwana su na tashi cikin kwanciyar hankali.
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wannan raddi ne ga sharhin ra’ayoyin jaridun THISDAY da Daily Trust, waɗanda su ka ɗora laifin kashe-kashen da ke faruwa a jihar Benuwai kan rashin ɗaukar matsalar da muhimmanci da Gwamnatin Tarayya ta ƙi yi.
Makonni biyu da suka gabata ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro su kawo ƙarshen zubar da jinin faɗan ƙabilanci.
Shugaba Muhammadu ya yi tir da mummunan rikicin ƙabilancin da ya ɓarke a cikin wasu ƙabilu a Jihar Benuwai.
Sannan kuma ya yi gargaɗin a gaggauta hana watsuwar kashe-kashen, tare da yin kira ga jami’an sojoji, DSS da ‘yan sanda su gaggauta hana ci gaban kashe-kashen.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Buhari, Garba Shehu ya fitar, Buhari ya umarci a yi duk wani ƙoƙarin da za a iya yi domin a shawo kan ɓarnar. Ya ce “kashe-kashen ya yi muni.”
Akwai rahotannin da ke nuna cewa an kashe sama da mutum 80 a yankunan Umogidi da ke Entekpa-Adoka na cikin Ƙaramar Hukumar Otukpo.
Haka kuma wasu rahotannin sun tabbatar da kisan wasu mutum 34 a ƙauyen Mgaban da ke Ƙaramar Hukumar Benuwai ta Arewa a ranar Juma’a.
Shugaba Buhari ya yi tir da irin ta’addancin da ake yi a rikice-rikicen ƙabilanci.
Sannan Buhari ya umarci jami’an tsaro su gano waɗanda su ka yi kisan, su kamo su sannan su gurfanar da su a kotu, domin a hukunta su.
“Shugaba Buhari ya na taya iyalan waɗanda aka kashe jima da ta’aziyya. Kuma ya bada umarnin sake duba yadda yanayin tsaron yankin ya ke, tare da tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.”