Tsohon Sanata Dono Melaye, ɗan siyasar da ba ya barin ta-kwana, ya maida wa Gwamna Nysome Wike na Ribas kakkausan raddi, dangane da furucin gwamnan cewa Dino Melaye ba shi da kimtsi, kamun-kai da natsuwar da zai zama gwamna.
A martanin da Dino ya mayar masa, ya ce, “Wike ya ma fi kowa sanin cewa na cancanta. Domin da na fito takarar gwamna ma a 2019, sai da Wike ya ba ni gudunmawar dala 220,000.
“Sannan kuma ya sa aka ɗauke ni a jirgin sa daga Fatakwal har Kogi, aka ajiye ni, a ranar zaɓen fidda-gwani. Kuma lokacin zaɓen ya yi ta kira na don ya ji halin da muke ciki.” Cewar Dino, a wata hira da gidan talabijin na AIT.
Dino ya ce Wike ya na jin haushin sa ne saboda ya ƙi goyon bayan ajendar sa a takarar zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a PDP.
Na Fi Wike Cancantar Zama Gwamna:
“Ya kamata mutane su tuna ni ba sabon yanka raken ɗan siyasa ba ne. Na yi Wakilin Majalisar Tarayya, kuma na yi Sanata sau biyu. Kuma na yi hadimin shugaban ƙasa. Shi kuwa Wike duk bai yi waɗannan muƙaman ba.
Melaye ya ce dama ba ya neman goyon bayan Wike dangane da takarar gwamnan da ya ke yi a Kogi.
“A jihar Osun Wike bai goyi bayan Adeleke na PDP, amma kuma Adeleke dai ne ya yi nasarar zama gwamna.
“Ɗan takarar da Wike ya goyi baya a Cross River ya faɗi zaɓe.”
“A Akwa Ibom Wike bai goyi bayan ɗan takarar PDP ba, ya goyi bayan mai adawa da PDP, wato Albert, Kuma faɗuwa zaɓe ya yi. Gwamnonin Benuwai da Abiya na Enugu sun fito takarar sanata, Wike ya goya masu baya, amma duk ba su ci zaɓe ba.” Cewar Dino.
A ƙarshe ya shawarci Wike cewa ya na ba shi shawara duk lokacin da ya sha ya yi mankas, to ya kiyayi yin magana. “Saboda baki ya san abin da zai faɗa, amma bai san abin da za’a mayar masa martani ba.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Gwamna Wike ya ce Dino Melaye ba shi da natsuwa, kimtsi da kamun kan da zai riƙe muƙamin gwamna.
Gwamna Nysome Wike na Jihar Ribas ya ce tunanin da Dino Melaye ke yi na zama gwamna a Jihar Kogi, abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba, saboda ba shi da kimtsi, natsuwa da kamun-kai da har za a amince a ba shi mulkin jiha sukutum.
Melaye wanda ya yi wa PDP Kakakin Yaɗa Labarai na Kamfen ɗin Zaɓen Shugaban Ƙasa, ya fara fafutikar neman zaɓen fidda-gwani na PDP a zaɓen gwamna da za a yi ranar 11 Ga Nuwamba a Kogi
Da ya ke magana cikin gungun ‘yan jarida ranar Talata a Patakwal, babban birnin Jihar Ribas, Wike ya ce ya na sane da irin ƙulle-ƙullen da PDP ke yi domin ta murɗe zaɓen fidda-gwani, ta bai wa Dino Melaye takarar gwamna a Kogi.
“Haba jama’a, Allah na tuba, ai Dino Melaye ba shi da kimtsuwa, kamun kai da natsuwar da zai zama gwamna kwata-kwata. Ai gwamna ba wasan kwaikwayo ba ne da zai fito a hasko shi a fim ko talbijin. Mu na da magana kan mulki ne, ba wasan kwaikwayo ba.” Inji Wike.
“Don me PDP ke shirin murɗe zaɓen fidda-gwani ta bai wa Dino Takara? Ai ta san dai idan ta bai wa Dino takarar gwamnan Kogi, to ta faɗi zaɓe kai-tsaye.
“Don me ‘yan Kogi za su ce za su zaɓi Dino? Me ya sa za mu maida gwamna kamar wasan ‘yan tashe ne?”
Wike ya ce idan PDP ta tsayar da Dino ɗan takarar gwamna a zaɓen Nuwamba, to idan an faɗi zaɓe kada wani maras kunya ya fito ya ce an yi wa PDP maguɗi, saboda dai tun farko PDP ba ta haɗa ƙwarya da abokin burmin ta ba.
Dino kuma ya yi wa Wike gorin karatu mai zurfi, inda ya ce shi ya na da digiri biyar, amma Wike ba komai ba ne sai gatarin-gwari, wanda ba a komai da shi daga saran ita ce sai jifar burgu da tsuntsaye.
Discussion about this post