A yanayin ƙaramar jiha mai ƙananan hukimomi 14 kamar Zamfara, wacce ba ta da wata hanyar samun kuɗin shiga sai zaman tsammanin jiran kason kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya, masu sharhi na ganin cewa naɗa kwamishinoni har 26 a ma’aikatu 26, almubazzaranci ne kawai.
A zaɓen gwamnonin 2023, babu ɗan takarar da aka yi wa taron dangin gaggan tsoffin turaye, tsoffin kuraye da guma-guman tsoffin ‘yan alewa, kamar irin yadda aka yi wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal na PDP.
Dauda Lawan ya yi damben da ba a taɓa ganin sabon-yanka-raken ɗan siyasa ya yi irin sa kuma ya yi nasara ba.
Dauda ya buge ‘Shagon Maradun’, Gwamna Bello Matawalle. Kuma ya buge ‘Shagon Bakura’, Sanata Ahmed Sani Yarima. Sannan ya tattake ‘Shagon Mafara’, Abdul’aziz Yari, kuma ya buge ‘Shagon Shinkafi’, Mamuda Aliyu, waɗanda su huɗun su ka yi masa taron dangi, amma duk sai da ya yi masu kakkaɓar-‘ya’yan-kaɗanya.’
A ce ka na sabon ɗan siyasa, amma ka kayar da gungun tsoffin gwamnoni uku tare da Gwamna da ke kan mulki, zai yi wuya a ce akwai bajintar da ta fi wannan a siyasa.
Sauran waɗanda su ka yi masa taron-dangi har da sanatoci da mambonin tarayya da ke kan kujera, kai da duk wani gadagurun wane da wane ko wane ɗan wanen Zamfara.
Sai dai kuma wannan nasara da ya samu, za a iya cewa murnar ta ɗan taƙaitaccen lokaci ne, idan aka yi la’akari da irin manya-manyan ƙalubalen da ke gaban Gwamna Mai Jiran Gado, Dauda Lawal. Daga ranar da za a rantsar da shi a 29 ga Mayu, 2023, to daga ranar ce zai gane cewa lallai ya ɗauko Dala ba gammo.
Dauda Lawal Da Ƙalubalen Talauci Da Yunwa A Zamfara:
Hukumar Ƙididdigat Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS), wadda mallakar Gwamnatin Tarayya ce, ta ce kashi 78 bisa 100 na al’ummar jihar duk matalauta ne. Noman da jihar ke tutiya da shi, yanzu tuni ya samu cikas, sakamakon ‘yan bindigar da su ka ragargaje Zamfara.
Rahoton 2021 da IFRC ta fitar ya ce mutum milyan 2.53 ne daga Arewa maso Yamma ciki har da Zamfara, Katsina da Sakkwato da Katsina, duk za su fuskanci tsananin yunwa da ƙarancin abinci, sadadiyyar hare-haren ‘yan bindiga.
BudgiT ta fitar n Zamfara ce ta 32 a jerin sunayen jihohin da ke fama da talauci, tantagaryar sa.
Kashi 80 bisa 100 na al’ummar Zamfara manoma ne. Amma saboda tsananin bala’in hare-haren ‘yan ta’adda ya sa manoma da sauran talakawa an gudu daga yankunan karkara.
Daga 2019 zuwa 2021 rahoto ya ce Zamfara ba ta tsinana wani abin tasiri ga tattalin arzikin jihar ba.
Kasancewar sa ƙwararren ma’aikacin banki, ana kyautata wa Dauda Lawal zaton zai gaggaci masu zuba jari zuwa Zamfara, wanda yin hakan zai samar wa ɗimbin matasa masu zauna-gari-banza za su samu aikin yi.
Wata matsala ita ce matsalar rashin ingantattun kasuwanni. Idan ka cire Babbar Kasuwa Gusau, to dukkan sauran su na buƙatar a inganta su, ko ma a sake gina su baki ɗaya.
Dauda Lawal Da Ƙalubalen Matsalar Tsaro:
Wani rahoton da jihar ta fitar ya ce tsakanin 2011 zuwa 2019, an yi garkuwa mutum 3,672, sannan an biya kuɗin fansa har Naira biliyan 3. An bar mata da ƙananan yara 4,983, waɗanda aka kashe mazajen su ko iyayen su. An maida ƙananan yara 25,050 marayu. Mutum 190,340 sun rasa gidajen su.
Lamari ya ƙara lalacewa, ta yadda yanzu mahara su na kai hari cikin manyan garuruwan Zamfara, irin su Gusau, Kaura Namoda da Talata Mafara.
Ya zama wajibi gwamna mai jiran gado idan ya hau, ya bijiro da hanyoyin kawo ƙarshen rikicin jihar Zamfara, wanda tilas ya samar da fahimtar juna tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa musamman a yankunan karkara.
Sannan akwai buƙatar inganta ilmi, kiwon lafiya da sauran su. Kasancewar a jihar Zamfara ce aka fi samun mutuwar jirajirai a ƙasar nan, kamar yadda rahoto ya tabbatar a cikin 2020. A cikin jarirai 100,000, aƙalla 576 ke mutuwa a Zamfara. A ƙasar nan kuwa aƙalla 197 ke mutuwa a cikin 100,000.
Dauda Lawal zai fuskanci ƙalubalen matsalar likitoci da ƙarancin asibitoci.
Matsalar ilmi kuwa ita ma zaune ta ke da gindin ta a Zamfara.UNESCO ta ce akwai yara masu gararamba ba su zuwa makaranta har 883,952.
Matsalar bashi ma gagarimar abu ce a Zamfara. DMO ta ce zuwa Disamba 2022, ana bin Gwamnatin Zamfara bashin Naira 112,197,059,996. Wannan fa bashin cikin gida ne kaɗai. Na waje kuwa ana bin Najeriya bashin N28,861,053.
“Cikin 2022, kashi 45.9 na kuɗaɗen da Zamfara ta kashe, duk a biyan bashi su ka tafi. Sauran kashi 54.1 kuma wajen biyan albashi, kuɗaɗen ‘yan fansho, tafiyar da ofisoshi da wasu ‘yan ayyukan raya ƙasa da ba a rasa ba. Wannan kuma babbar kasada ce,” inji Mohammed.
A matsalar ilmi, Hukumar Jarabawar NECO na bin Jihar Zamfara bashin naira biliyan 1.3. na NECO da WAEC. Akwai buƙatar Lawal ya iya biyan kuɗaɗen, domin a fito wa ɗaliban da sakamakon su.
Saboda a 2022 Jihar Zamfara ba ta yaye ɗalibin sakandare ko ɗaya a jarabawar WASSCE, saboda ba a biya masu kuɗin jarabawar ba.
Ma’aikata sun yi wa jihar yawa. Jiha mai ƙananan hukumomi 14, amma kwamishinoni da ma’aikatu har 26. Sannan babu wata hanyar samun kuɗaɗen shiga, sai an jira kuɗaɗen kason Gwamnantin Tarayya, wannan ganganci ne da almubazzaranci.