Kwana ɗaya bayan Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed ya furta kalaman da su ka sha bamban da na Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC kan dalilin rashin aika sakamakon zaɓe cikin Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta iReV, Ministan ya sake waskewa, amma a wannan karon ɗora laifin kasassaɓar da ya yi ne kan ‘yan jarida.
Lai ya ce ‘yan rahoto ne ba su aika bayanan da ya yi a daidai da abin da ya furta ba.
PREMIUM TIMES ta ruwaito Lai ya ce INEC ta ɗauki matakin ƙin aika sakamakon zaɓe daga Na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Zaɓe, wato BVAS zuwa cikin Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta iReV, saboda ta gano cewa ‘yan dandatsa na ƙoƙarin shiga manhajar domin su baddala sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa, wanda aka yi a ranar 25 ga Fabrairu.
“INEC sun yi zargin ‘yan dandatsa na ƙoƙarin yin shigar-kutse, wato ‘hanking’ a cikin manhajar iReV ta yanar gizo domin su baddala sakamakon zaɓen.” Cewar Ministan Harkokin Yaɗa Labarai, Lai Mohammed.
Ma’anar kalaman da Lai ya yi su na nufin INEC ta na sane ta ƙi tura sakamakon zaɓe daga BVAS kai tsaye zuwa cikin iReV, saboda ta na zargin za a baddala sakamakon.
Sai dai kuma maganar da Lai ta yi ta Sha bamban da dalilan da INEC ɗin da kan ta ta bayyana.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ya ce INEC ta samu lattin aika sakamakon zaɓe cikin iReV, saboda cikas ɗin na’urorin aiki, ba saboda gudun yunƙurin da wasu ke yi na yi wa sakamakon maƙarƙashiya ba.
Sai dai kuma ranar Laraba Lai ya zargi ‘yan jarida, musamman PREMIUM TIMES da cewa ta buga bayanin sa ba daidai ba.
Wancan bayani da Lai ya yi a ranar Laraba, a lokacin ya na Washington DC, Amurka.
Discussion about this post