Wasu malaman addini sun yi tir da yadda zina tsakanin ƴaƴa musamman mata ke ci gaba da yawaita a tsakanin a fadin kasar nan.
Malaman da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a jihar Legas ranar Juma’a sun bayyana haka a matsayin abu mafi muni da ya ke neman dagula gidajen mutane.
Fasto Peter Ayeni na cocin ‘Victory of God Mission’ a Ayobo-Ipaja ya ce zina tsakanin ‘ya da mahaifinta babban zunubi a addinance.
“ Lalata tsakanin ‘ya da mahaifinta ba fasikanci ko wani abu mara kyau ba ne kawai a bin kyama ce sannan zunubi ne mai girman gaske.
Ya ce akwai wasu iyaye maza dake dirka wa ‘ya’yan su mata ciki.
Ayeni ya ce haka na cutar da kwakwalwa da rayuwar yarinyar har ta koma.ga mahaliccinta.
Ya ce akwai la’anar da ke kan mahaifin da ya sadu ‘yar cikinsa a abinda yafi dace wa garesa shine neman tuba da kuma addu’a ta musamman domin Allah ya shirye shi.
Ayeni ya yi kira ga iyaye mata da su rika magana sannan suna tona asirin mazajen su a duk Lokacin da suka yi lalata da ‘ya’yan su mata.
“Da dama daga cikin matan dake boye irin wannan kazantar na yin haka ne saboda kada auren su ya mutu ko kuma tsoron mazajen nasu ta hanyar barazanar kisa ko wani abin.
Ya ce kamata ya yi iyaye su rika wayar da kan ‘ya’yansu kan saduwa tsakanin namiji da mace da wanda ya dace da wanda bai dace ba sannan su karfafa gwiwowin ‘ya’yan kan su tona asiri da sanar da wani a duk Lokacin da abu irin haka ya auku da su.
Ya Yi kira ga gwamnati da ta kara tsawaita hukuncin masu yin lalata da ‘ya’yan su domin zama abin gargaɗ ga sauran mutane.
“Shan giya, kadaici, mutuwar aure, rashin saduwa da mace na daga cikin dalilan dake kawo haka.
Bayan haka wani limami mai suna Mukaila Lawal shima ya a nashi jawabin ya yi tir da wannan aika-aika da iyaye ke aikatawa da ƴaƴan su mata.
“Akan wani dalili ne zai sa mahaifi zai yi lalata da ‘yar cikinsa? Duk mai aikata irin haka na bukatan a kai shi asibitin mahaukata a duba kwakwalwarsa domin babu lafiya a cikin sa.
Lawal ya yi kira ga iyaye mata da su tabbatar ‘ya’yan su mata suna saka kayan da rashin ka rufe jiki ba irin wadanda zai ri bayyana jikin su ba wadda zai rika ba maza sha’awa har su rika tunanin lalata da su ba.
Discussion about this post