Kwamitin Binciken Salwantar Maƙudan Kuɗaɗe ya gayyaci Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed su bayyana domin su yi bayanin yadda aka yi har Ofishin Ministan Shari’a ya amince a biya wasu ‘yan kwangilar da ba a san ko su wa ba ne, har dala miliyan 200.
Kwamitin ya yi barazanar cewa ba sau ɗaya ba ya gayyace su, amma sun ƙi bayyana, saboda haka zai umarci a kamo ‘yan kwangilar da aka ce an bai wa kuɗaɗen da kuma ministocin biyu.
Tun da farko dai wani ne ya tsegunta wa Hukumar Sa-ido Kan Hada-hadar Kuɗaɗen Gwamnati (NFIU) cewa an biya wasu kamfanonin bogi har dala miliyan 200 matsayin wai sun yi aikin tuntuɓa, bisa amincewar Ofishin Ministan Shari’a da kuma Shugaba Muhammadu Buhari.
Mai tsegumin, wato ‘whistleblower’, ya ce an biya kuɗaɗen a kamfanoni biyu, kamar yadda Shugaban Kwamitin Majalisa, Mark Gbillah daga Jihar Benuwai ya bayyana.
An dai aika wa Ministar Kuɗaɗe Zainab da Ministan Shari’a Malami sammacin gayyata tun a ranar Laraba, amma har yau ba su hallara ba.
Kamfanonin masu suna ‘Biz Plus’ da ‘GSCL’ wai sun karɓi dala miliyan 200 bisa umarni da amincewar Minista Malami.
Shugaban Kwamiti ya ce su na zargin sace kuɗaɗen aka yi kawai, domin ta Ofishin Ministan Shari’a aka karkatar da kuɗaɗen, alhali ba shi da ikon kashe wa Najeriya kuɗaɗe, ko ikon bada umarnin a kashe kuɗaɗen Najeriya, saboda doka ba ta ba shi wannan ƙarfin ikon ba.
“Saboda haka mu ke buƙatar bayyanar Ministar Harkokin Kuɗaɗe da Ministan Harkokin Shari’a su zo su yi mana bayanin yadda aka karkatar da waɗannan maƙudan kuɗaɗen, waɗanda wani mai kwarmato ya bayyana cewa an karkatar dasu bisa iznin Munsita Malami.
Cikin Disamba 2022 sai da Majalisa ta yanke shawarar binciken salwantar gangar ɗanyen mai miliyan 48 da aka haƙƙaƙe wasu manyan ‘yan ƙaƙudubar Najeriya sun sayar a Chana.